Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000 A Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙaddamar da shirin rabon takin noma kyauta na daminar shekarar 2026 ga manoma ƙanana 150,000 a faɗin jihar, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce zai ƙara bunƙasa harkar noma da tabbatar da wadatar abinci.
An ƙaddamar da shirin ne a Dandalin Murtala Square da ke Kaduna, inda gwamnatin ta sanar da rabon manyan motoci 500 na takin zamani tare da faɗaɗa tallafin amfani da injinan noma domin sauƙaƙa ayyukan noma ga manoma.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa shirin na daga cikin manufofinta na ƙarfafa samar da abinci, rage tsadar noma da kuma inganta tattalin arziƙin al’ummomin karkara ta hanyar bai wa manoma kayan aikin da za su taimaka musu wajen ƙara yawan amfanin gona.
A cewar gwamnatin, samar da taki da injinan noma a kan lokaci zai taimaka wajen haɓaka noman zamani, ƙara yawan amfanin gona da kuma bai wa manoma damar shawo kan matsalolin hauhawar farashin kayan noma da ƙalubalen sauyin yanayi.
Har ila yau, gwamnatin ta bayyana cewa irin wannan gagarumin tallafi bai taɓa samuwa ba a tarihin Jihar Kaduna, tana mai tunatar da cewa a shekarar 2024 an raba manyan motoci 500 na taki, yayin da a shekarar 2025 aka sake rabon manyan motoci 400, lamarin da ta ce ya taimaka wajen haɓaka yawan amfanin gona a sassa daban-daban na jihar.
Gwamnatin ta ƙara da cewa rabon takin bana na shekarar 2026 ya zo ne domin ci gaba da gina nasarorin da aka samu a shekarun baya, tare da ƙarfafa samar da isasshen abinci da bunƙasa harkar noma a faɗin Jihar Kaduna.
