<span></span>
Ƙasashen China da Rasha sun sanar a ranar Lahadi cewa za su gudanar da atisayen haɗin gwiwa na rundunar sojin ruwa na shekara-shekara a gaɓar Tekun China.
Ƙasashen biyu na da alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki mai ƙarfi, wadda ke ƙara ƙarfafa saboda adawarsu da tsarin siyasar duniya da suke ganin Amurka ce ta mamaye shi.
A cikin ’yan shekarun nan, sojojin China da na Rasha sun riƙa gudanar da atisayen soja na haɗin gwiwa akai-akai, lamarin da ƙasashen Yamma da wasu ƙasashe ke nuna damuwa, musamman tun bayan mamayar da Rasha ta kai Ukraine a shekarar 2022.
Ma’aikatar Tsaron China ta bayyana cewa rundunonin ruwa na ƙasashen biyu za su gudanar da atisayen haɗin gwiwa na “Joint Sea-2026” a ruwa da sararin samaniyar da ke kusa da birnin Qingdao, wanda ke gabashin China kuma ɗaya ne daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwan sojin ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan kammala atisayen, wasu daga cikin rundunonin ƙasashen biyu za su gudanar da sintirin haɗin gwiwa a wasu sassan Tekun Pacific, domin fuskantar barazanar tsaro tare da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Rundunar Yankin Arewa ta sojojin China ta ce za ta tura jiragen ruwa masu linzami guda biyu, jirgin ruwa mai rakiyar yaƙi guda ɗaya, jirgin ruwa mai nutsewa ƙarƙashin teku (submarine), jirgin samar da kayan aiki da kuma jirgin ceto.
Ta kuma tabbatar da cewa dukkan jiragen da za su halarci atisayen sun riga sun isa Qingdao.
A cewar sanarwar, atisayen zai haɗa da ayyukan leƙen asiri, kariya daga hare-haren sama da makamai masu linzami, da kuma hare-haren kan jiragen ruwa.
A nata ɓangaren, Rundunar Tekun Pacific ta Rasha ta ce atisayen zai gudana daga 6 zuwa 13 ga Yuli a Tekun Yellow, wanda ke tsakanin China da yankin Koriya.
Ta ce atisayen zai kuma ƙunshi ayyukan ceto na haɗin gwiwa, yaƙi da jiragen ruwa masu nutsewa, kariyar sararin samaniya da kuma atisayen harba manyan bindigogi.
Rasha ta kuma bayyana cewa ta tura wani babban jirgin yaƙi, jirgin rakiya, jirgin ruwa mai nutsewa mai amfani da dizal da kuma jirgin ceto zuwa tashar Qingdao domin halartar atisayen.
Mataimakin babban kwamandan rundunar sojin ruwan Rasha, Rear Admiral Sergei Sinko, ya ce manufar atisayen haɗin gwiwar ita ce ƙara ƙarfafa dabarun tsaro tsakanin ƙasashen biyu da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Atisayen na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan ziyarar da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya kai China, inda shi da Shugaban China, Xi Jinping, suka jaddada ƙudirin ci gaba da ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashensu.
