Rodri Ya Amince Da Tayin Komawa Real Madrid
Rahotanni sun ce ɗan wasan tsakiyar Manchester City, Rodri, ya amince da tayin komawa Real Madrid, yayin da tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin biyu ke ci gaba da ƙarfi.
Rodri, mai shekaru 30, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan da Manchester City ta dogara da su tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Atletico Madrid a shekarar 2019 kan kuɗi fam miliyan 62.6.
Tun daga lokacin, ya buga kusan wasanni 300 a City, inda ya taimaka matuƙa wajen nasarorin da ƙungiyar ta samu a cikin ‘yan shekarun nan.
Haka kuma, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun ‘yan wasan tsakiya a Ingila da ma duniya baki ɗaya.
Kwangilarsa da Manchester City za ta ƙare a shekarar 2027.
A cewar ɗan jarida Matteo Moretto, Rodri ya cimma yarjejeniya da Real Madrid, kuma yanzu ana jiran ƙungiyoyin biyu su cimma matsaya kan cinikin.
Rahoton ya ce Rodri ya daɗe yana sha’awar koma wa Real Madrid, yayin da ƙungiyar ta Spain ke fatan ɗaukarsa kan kuɗin da ba su yi yawa ba, kasancewar ya rage masa shekara biyu a kwantiraginsa.
Idan cinikin ya kammala, Manchester City za ta fuskanci ƙalubalen sake tsara tsakiyar fili, musamman bayan ficewar Bernardo Silva.
A gefe guda kuma, zuwan Rodri zai ƙara wa Real Madrid ƙarfi a tsakiyar fili yayin da ƙungiyar ke ƙoƙarin komawa kan ganiyarta bayan kakar wasan da ta gabata da ta ƙare ba tare da lashe wani kofi ba.
