<span></span>
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka ce mafi girman nasarar da ɗan Adam ya taɓa samu a tarihi yayin da ƙasar ke bikin cika shekara 250 da kafuwa.
A yayin jawabin nasa na tsawon mintuna 45, Trump ya kuma sake sukar abokan adawarsa na cikin gida waɗanda ya bayyana a matsayin ’yan kwaminisanci.
An dai jinkirta jawabinsa na sa’o’i da dama a sakamakon guguwar iska da ruwan sama suka tilasta kwashe jama’ar da suka taru a birnin Washington domin sauraron jawaban.
Da yake jawabi a gaban dubban mutane a filin taro na National Mall, Trump ya ce Amurka a ƙarƙashin mulkinsa ta fi kowane lokaci alfahari da kanta.
“Tsawon shekaru 250, jamhuriyar Amurka ta kasance mafi girman nasarar da ɗan Adam ya taɓa samu,” in ji Trump.
Ya kuma yaba wa tsoffin sojojin da suka yi yaƙe-yaƙen Duniya na Biyu, Koriya da Vietnam, yana mai cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da kwaminisanci.
Sai dai daga bisani ya sake sukar masu adawa da tsarin siyasar Amurka, inda ya bayyana cewa ba za su bari kwaminisanci ya samu gindin zama ba a ƙasar.
Trump ya kuma yi iƙirarin cewa gwamnatinsa ta samu manyan nasarori a hare-haren soji da aka kai kan Iran da Venezuela.
Ana dai gudanar da bikin ne yayin da zafin rana ya kai matsayi mafi tsanani a birnin Washington, inda aka samu yanayin zafi ya kai digiri 39.4 a ma’aunin Celsius a ranar 4 ga Yuli.
Haka kuma, guguwar iska da ruwan sama sun kawo cikas a wasu bukukuwan da aka shirya a biranen New York, Philadelphia da Boston.
Sai dai wani binciken jin ra’ayin jama’a da Jami’ar Quinnipiac ta gudanar ya nuna cewa kashi 61 cikin 100 na Amurkawa na ganin ƙasar ba ta cika manufofin da aka bayyana a Takardar Ayyana ’Yancin Kai ta shekarar 1776 ba.
