<span></span>
Ƙungiyar Real Madrid ta sanar da ɗaukar ɗan wasan baya na ƙasar Netherlands, Denzel Dumfries, daga Inter Milan kan kuɗi kusan Yuro miliyan 20 — kimanin dala miliyan 23.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi, ta ce ta cimma yarjejeniya da Dumfries, wanda ya sanya hannu kan kwantiragin shekara huɗu da zai zaunar da shi a Santiago Bernabeu har zuwa 30 ga Yunin 2030.
Dumfries, mai shekara 30, wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan baya na gefen dama, ya wakilci ƙasar Netherlands a Gasar Kofin Duniya, kafin Morocco ta fitar da su a zagayen ’yan 32 a bugun fenariti.
Zuwansa Real Madrid zai ƙara fafatawa domin ƙwatar riga tare da ɗan wasan Ingila, Trent Alexander-Arnold, wanda shi ma yake buga lambar baya a gefen dama.
Dumfries ya koma Inter Milan ne daga PSV Eindhoven a shekarar 2021, inda ya lashe kofunan Serie A biyu, sannan ya kai wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai ta Champions League sau biyu tare da ƙungiyar ta Italiya.
Shi ne ɗan wasa na huɗu da Real Madrid ta saya a wannan bazara, bayan Marc Cucurella, Bernardo Silva da Ibrahima Konate.
Real Madrid na ci gaba da sake fasalin tawagarta bayan ta ɗauki tsohon kocin Portugal, Jose Mourinho, domin maye gurbin Alvaro Arbeloa, bayan da ƙungiyar ta shafe kakar wasa biyu ba tare da lashe wani babban kofi ba.
Haka kuma, Real Madrid ta tsawaita kwantiragin ɗan bayanta Antonio Rudiger zuwa shekarar 2027, bayan Dani Carvajal da David Alaba sun bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan da ta gabata.
