<span>Peter Obi</span>
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Peter Obi ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi iyakacin ƙokarinsa wajen magance matsalolin tsaron Najeriya, sai dai ya jaddada cewa ƙokarinsa ba ya wadatar da buƙatun ƙasar a halin yanzu.
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake maida martani kan kalaman Babban Jagoran Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, wanda kwanan nan ya ce Shugaban ƙasar ya yi iyakacin ƙokarinsa wajen daƙile rashin tsaro.
Yayin da yake magana a wata tattaunawa da ya yi da wani mai harkar yaɗa labarai, Chude Jideonwo Obi ya ce ya amince da ƙididdigar babban malamin addinin, sai dai ya kafa hujjar cewa ainihin batun shi ne ko ƙoƙarin na Tinubu ya samar da sakamakon da ake buƙata.
“Wani ya tambaye ni jiya, ya ce Fasto Adeboye ya ce Tinubu ya yi iyakacin ƙokarinsa kuma bai ji daɗi ba,” in ji Obi.
“Sai na ce, a’a Fasto Adeboye ya kasance uba a fannin addini mai cike da kwarjini da girmamawa, wanda na yi amanna da gaskiyarsa da kuma alherinsa.
“Kuma abin da ya faɗa daidai ne. Ya ce, ya yi iyakacin ƙokarinsa. Yana yin iyakacin ƙokarinsa. Shi ke nan. Shi ne amsar da ta dace.”
Kodayake, Obi ya nuna shakku kan tasirin ƙoƙarin Shugaban ƙasar, inda ya ce taɓarɓarewar tsaron ƙasar na nuni da gazawar shugabanci.
“Tambayar da ya kamata a yi ita ce: Shin iyakacin ƙokarinsa ya gamsar? Inda muka tsinci kanmu a yau, hakan ya shafi batun gwaninta da ma’aikata,” in ji shi.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya jaddada cewa, shugabanci na gari ya wuce batun yin ƙoƙari kawai, domin yana buƙatar gwaninta, jajircewa da kuma sadaukarwa.
“Idan ina magana a kan shugabanci, nakan ce gwaninta, jajircewa, tausayi, sadaukarwa, da kyakkyawan hali. Waɗannan ne batutuwan. Shugaba Tinubu ya gaji. Yana buƙatar ya tafi gida ya huta,” in ji Obi.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP ya yi waɗannan kalaman ne yayin da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa ya kamata ’yan Najeriya su marawa takararsa baya maimakon su marawa wani ɗan takarar adawa baya.
