<span></span>
Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da wani mai suna Ali Sulaiman Adam, ɗan unguwar Gadon Ƙaya, a Babbar Kotun Jihar Kano bisa zargin kashe matarsa, Maryam Nababa Badamasi tare da ƙona ɗakin da ya aikata laifin.
Ana tuhumar Ali da laifuka biyu da suka haɗa da kisan kai da kuma ƙona gida.
Sai dai bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
Lauyan gwamnati ya buƙaci kotun ta ɗage shari’ar domin gabatar da shaidu, yayin da lauyan wanda ake zargin ya nemi a ci gaba da ba shi belin da aka ba shi a baya.
Sai dai Alƙali Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 27 ga Yuli, domin sauraron sabon buƙatar beli da lauyan wanda ake zargin zai gabatar.
