<span></span>
A ranar Talatar makon nan ce abin da masu iya magana kan ce “ba a sanin maci tuwo sai miya ta ƙare” ya tabbata a kan tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa yayin da ta yi bankwana da Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Lamarin na zuwa ne bayan tawagar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta taka mata burki, yayin da doke ta da ci 2-0 a wasan kusa da na ƙarshe da suka fafata, duk da cewa Les Bleus ta kasance cikin tawagogin da suka fi ƙayatar da masu kallo tun farkon soma gasar.
Faransa dai tana sahun gaba cikin rukunin ƙasashen da aka yi hasashen za su lashe babbar gasar tamaular ta duniya, amma sai ga shi Sifaniya ta yi tumu-tumu da ita duk da irin zaƙaƙuran ’yan wasa da ta tara da har ake ganin ba ta da wani naƙasu a kowace lamba.
Tawagar wadda Didier Deschamps ke jagoranta ta zura ƙwallaye 16 a wasanni shida kafin karawar, amma ta kasa nuna irin wannan bajinta a yayin karawa da Sifaniya.
Sifaniya dai ta bai wa Faransa mamaki wadda take cike da dabaru na tsaron baya da kuma tsakiya irinsu Rodri da Dani Olmo da Fabian Ruiz, abin da ya hana zaƙaƙuran ’yan wasan Faransa taka rawar gaban hantsi.
Ƙwazon tsaron bayan tawagar Sifaniya ƙarƙashin jagorancin Luis de la Fuente ya kashe kaifin harin taurarin ’yan wasan Faransa a fafatawar.
An samu nasarar saka ƙwallon farko a raga ne a minti na 22 bayan da Lucas Digne ya yi wa shahararren matashin ɗan wasa Lamine Yamal ƙeta a cikin da’ira ta 18, kuma alƙalin wasa ya bayar da bugun fenariti, wanda Mikel Oyarzabal ya buga cikin natsuwa kuma ƙwallon ta wuce mai tsaron raga Mike Maignan.
Sifaniya ta saka ƙwallo ta biyu a minti na 58, lokacin da ɗan wasan baya na gefen dama Pedro Porro ya yi bajintar musayar ƙwallo da Dani Olmo, sannan ya zura ƙwallon a raga.
Kylian Mbappe da Ousmane Dembele sun gaza taɓuka komai a gaban masu tsaron bayan Sifaniya, waɗanda a halin yanzu suka kafa tarihin kiyaye ragarsu ba tare da an jefa ƙwallo ba har wasanni shida a gasar bana.
Da wannan nasara ta 2-0, La Roja ta tabbatar da gurbinta a wasan ƙarshe da za a yi a Filin Wasa na MetLife.
Kocin Sifaniya, Luis de la Fuente, ya ce nasarar ta samo asali ne daga tsayawa kan tsarin da suka gina tun kusan shekara huɗu da suka gabata, yana mai yaba wa ’yan wasansa bisa jajircewa, haɗin kai da kuma baiwar da suke da ita.
Abin da Mbappe da Deschamps suka ce
Kylian Mbappe ya amince cewa tawagarsa ba ta taka rawar da ake tsammani ba.
Mbappe ya ce duk da takaicin ficewar da suka yi, Faransa za ta sake tashi tsaye domin tunkarar ƙalubale na gaba, musamman Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai ta 2028.
“Ba mu yi abin da ya kamata ba, ta fuskar dabara da kuma yadda muka taka leda. Kuma muddin haka ta faru a wasan kusa da na ƙarshe na Kofin Duniya, ba za ka yi nasara ba,” in ji shi.
Shi ma Kociyan Faransa, Didier Deschamps, ya ce duk da rashin nasarar, yana alfahari da abin da ya cim ma tare da tawagar ƙasar tsawon shekarun da ya jagorance ta.
Deschamps, wanda ya lashe Kofin Duniya da Faransa a 2018 kuma ya kai ta wasan ƙarshe a 2022, ya ce lokaci bai yi ba na tattauna makomarsa.
Yadda wasan Argentina da Ingila ya kaya
Tun dai bayan tashi daga wasan Faransa da Sifaniya ne kuma hankula suka karkata zuwa birnin Atlanta domin fafatawa ta biyu a wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Ingila da Argentina.
Saura ƙiris ƙwallo ɗaya tilo ta raba gardama a wasan, wadda Anthony Gordon ya jefa ragar Argentina a minti na 55, bayan da Morgan Rogers ya sharo ta daga kusurwa, kuma Gordon ya shiga gidan Argentina ya taɓa ta faɗa raga.
Amma Enzo Fernandez ya farke wa Argentina ƙwallon a minti na 85, sannan Lautaro Martinez ya ƙara ta biyu ana daf da tashi, duk da taimakon Lionel Messi da ya gara wa kowannensu ƙwallayen da suka ci.
Da wannan nasara ta 2-1, Argentina za ta kara da Sifaniya a wasan ƙarshe a ranar Lahadi a New Jersey, yayin da Ingila da Faransa za su buga wasan neman na uku a ranar Asabar a Miami.
Sifaniya ta kai wasan ƙarshe ne bayan ta yi bajintar doke Faransa, lamarin da ya kawo ƙarshen burin Faransawa na lashe Kofin Duniya karo na uku.
An yi ɗokin ganin wasan Ingila da Argentina
Wasan Argentina da Ingila na ɗaya daga cikin manyan wasannin da aka yi ɗokin gani, kasancewar ƙasashen biyu na daga cikin ƙasashen da suka fi fice a tarihin ƙwallon ƙafa, baya ga tsohuwar taƙaddamar siyasa da ke tsakaninsu.
Argentina ƙarƙashin jagorancin Lionel Scaloni na neman zama ƙasa ta farko tun bayan Brazil a shekarar 1962 da za ta kare kambunta na Kofin Duniya sau biyu a jere.
Hakan kuma wannan gasar za ta kasance ta bankwana ga tauraron ƙwallon ƙafa, Lionel Messi, wanda ke da shekara 39 kuma ya zura ƙwallaye takwas a gasar zuwa yanzu.
Messi ya taka muhimmiyar rawa wajen kai Argentina wannan mataki, bayan ya jagoranci ƙasarsa wajen doke Cape Verde da Masar da a wasannin zagayen baya.
Sai dai Ingila wadda Thomas Tuchel ke jagoranta, ta soma wasan ne cike da ƙwarin gwiwa, inda Harry Kane da Jude Bellingham suka zura ƙwallaye 12 daga cikin 13 da tawagar ta ci a gasar.
Wannan shi ne karon farko da Argentina da Ingila suka haɗu a wata gasa tun bayan Kofin Duniya na 2002.
Tuchel ya ce duk da girman wasan, ba ya jin wani ƙarin matsin lamba, yana mai cewa ’yan wasansa na cike da ƙwazo da ɗokin fafatawa, inda ya bayar da tabbacin cewa Declan Rice, wanda ya yi fama da rashin lafiya, zai buga wasan.
Tawagar Three Lions dai ta kai wasan kusa da na ƙarshe na Kofin Duniya har sau biyu a cikin shekaru 60 da suka gabata, tun bayan lashe kofin a shekarar 1966 a filin wasa na Wembley— wato a gasar da aka yi a ƙasar Italy a 1990 da kuma a Rasha shekaru takwas da suka gabata.
Akwai tarihi mai zafi tsakanin Argentina da Ingila
Ɗaya daga cikin fitattun wasannin da ƙasashen biyu suka taɓa yi shi ne na kwata-fainal a Kofin Duniya na 1986 wanda aka buga a filin wasa na Estadio Azteca na Mexico City a ƙasar Mexico.
A wasan ne Argentina ta yi nasara da ci 2-1, sakamakon ƙwallayen Diego Maradona biyu, ciki har da fitacciyar ƙwallon da ya jefa raga da hannu wadda ake yi wa laƙabi da “Hand of God,” sai kuma wata ƙwallon ban mamaki da ya ci bayan ya yanke ’yan wasan Ingila.
Ɗan wasan tsakiyar Argentina Alexis Mac Allister ya ce Maradona na da matsayi na musamman a zukatan ’yan ƙasar, inda ya yi fatan ƙungiyar za ta sake maimaita nasarar da ta samu a 1986.
Ya kuma ce irin bajintar da Maradona ke nunawa abu ne da kusan babu mai iya yi, sai dai wataƙila Lionel Messi.
Sai dai kociyan tawagar, Lionel Scaloni ya yi ƙoƙarin kawar da siyasa daga wasan, inda ya ce abin da ya faru tsakanin ƙasashen biyu a baya tarihi ne mai raɗaɗi, amma wannan wasa ƙwallon ƙafa ne kawai, ba wani abu daban ba.
