Wane Ne Khalil Al-Hayya, Sabon Shugaban Kungiyar Hamas?
Tun da farko kan mambobin kwamitin zaben ya rabu kan wanda zai zama sabon shugaban kungiyar.
A zagayen farko na zaben ba a samu wanda ya yi nasara kai tsaye ba.
A cewar wani jami’in Falasdinawa mai masaniya kan zaben, tsohon shugaban ofishin siyasa na Hamas, Khaled Mashaal, ya samu kuri’u fiye da Al-Hayya, amma bai kai adadin kuri’un da ake bukata domin samun nasara kai tsaye ba.
Bisa ga dokokin Hamas, dole ne dan takara ya samu akalla kuri’u 36 daga kwamitin zaben mai mambobi 69.
An fahimci cewa zagaye na biyu na zaben ne ya tantance wanda ya yi nasara.
Wane ne Khalil al-Hayya?
An haifi Khalil al-Hayya ranar 5 ga watan Nuwamban 1960.
Ya samu digirinsa na farko a jami’ar Musulunci da ke Gaza, yayin da ya samu digirinsa na biyu a Jami’ar Jordan.
Sannan ya samu digirin digirgir a jami’ar Kur’ani da ilimin Addinin Musulunci.
Ya shiga Hamas ne bayan kammala digirinsa na farko a lokacin yana aiki a matsayin malamin makaranta.
Ya rike mukamai a kungiyar har zuwa matsayin babban mataimakin sashen siyasar kungiyar, mukamin da ya rike har zuwa Agustan 2024.
Al-Hayya, wanda a baya ya kasance jagoran kungiyar Hamas a kasashen waje, ana kallonsa cikin masu tsattsauran ra’ayi a Hamas, wanda ya fito fili a lokacin yakin Isra’ila da Hamas da ya fara kusan shekaru uku da suka gabata.
Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin amintattun mutane na kusa ga tsohon shugaban Hamas, Yahya Sinwar, kuma an bayyana shi a matsayin “daya daga cikin tsirarun mutanen da Sinwar yake ji da su.”
Bayan kashe Yahya Sinwar a watan Oktoban 2024, an rika kallon Al Hayya a matsayin daya daga cikin wadanda za su iya maye gurbinsa a shugabancin kungiyar.
Wace rawa ya taka a Hamas?
A matsayinsa na babban mai shiga tsakani a tattaunawar Hamas, al-Hayya ya samu karbuwa a idon duniya ta hanyar jagorantar tawagogin kungiyar a tattaunawar tsagaita wuta, inda ya rika ganawa da masu shiga tsakani daga Masar da Katar.
A baya-bayan nan ya kasance babban jami’in diplomasiyyar da tsare-tsare siyasar.
A watan Nuwamban 2019, Al Hayya da Rouhi Mushtaha suka jagoranci wata tawaga daga Gaza, zuwa kasashe da dama, ciki har da Turkiyya da Lebanon.
Al Hayya ya kuma jagoranci tattaunawar sulhu da kungiyar Fatah.
A watan Janairun 2022, ya ziyarci Aljeriya bayan ya samu gayyata daga shugaban kasar Aljeriya.
Al Hayya ya wakilci Hamas a tattaunawar da aka yi da Isra’ila kan sakin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta.
Ya sha tsallake rijiya da baya
A watan Satumban 2025, Al-Hayya mai shekara 65 ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas da ke wani taro a Doha, babban birnin Katar.
A lokacin harin an kashe mutum biyar ciki har da dansa, wanda mamba ne a rundunar tsaron Katar.
A lokacin, Firaministan Isra’ila ya ce an kai musu harin ne saboda zarginsu da kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a kudancin Isra’ila, wanda ya haifar da yakin Gaza.
Da fari an kashe wasu ‘ya’yan Al-Hayya biyu a wani hari da aka kai da nufin halaka shi a Gaza, yayin da aka kashe dansa na hudu a wani hari a Gaza cikin watan Mayun da ya gabata.
A 2007 ne wani harin Isra’ila kan gidansa ya kashe bakwai daga cikin ‘yan’uwansa, ciki har da shakikansa biyu.
Haka ma a 2008 aka kashe daya daga cikin ‘ya’yansa a wani hari ta sama da aka kai masa.
Sannan a 2014 aka kashe wani dan nasa da surukarsa da kuma jikansa a wani hari ta sama
