<span></span>
Majalisar Turai (Council of Europe) ta buƙaci Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta ƙara ɗaukar matakan kare martaba da sahihancin wasan ƙwallon ƙafa.
Majalisar ta bayyana cewa Gasar Kofin Duniya ta 2026 ta jefa ayar tambayoyi masu yawa kan yadda ake tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa.
A cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na Majalisar, Alain Berset, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce gasar a wannan karo ta fuskanci ƙalubale da suka haɗa da katsalandan daga bakin siyasa, cin zarafin ’yan wasa ta hanyar wariyar launin fata da kuma faɗaɗa harkokin caca, lamarin da zai iya ƙara haɗarin maguɗin sakamakon wasanni.
Ya ce duk da cewa gasar za ta ƙare ne da wasan ƙarshe tsakanin Argentina da Sifaniya, tambayoyin da ta haifar ba za su ƙare da busar ƙarshe ba.
“Gasar za ta ƙare yau [Lahadi]amma cece-kucen da ta haifar ba za su ƙare ba,” in ji Berset.
Ya buƙaci FIFA ta fara tattaunawa da nazari tun daga yanzu domin gina ingantaccen tsarin da zai kare martabar Gasar Kofin Duniya ta 2030.
Berset ya kuma soki abin da ya kira tsoma bakin siyasa cikin harkokin ƙwallon ƙafa, yana mai nuni da roƙon da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa shugaban FIFA Gianni Infantino na a sake duba dakatarwar da aka yi wa ɗan wasan Amurka Folarin Balogun.
Ya ce idan ana sauya ƙa’idoji saboda matsin lamba, hakan na iya jefa sahihancin sakamakon wasanni cikin shakku.
Haka kuma ya nuna damuwa kan matakin FIFA na karɓar kamfanin hasashen caca ADI Predictstreet a matsayin abokin hulɗa a karon farko.
A cewarsa, caca ba ta tsaya kan hasashen wanda zai ci wasa ba, har ta kai ga hasashen abubuwan da ɗan wasa zai yi a cikin wasa, abin da ya ce na iya buɗe ƙofar maguɗi da shirya sakamakon wasanni.
Majalisar Turai ta ce ya zama wajibi a fara ɗaukar matakan kare martabar wasanni tun daga yanzu, domin tabbatar da cewa Gasar Kofin Duniya ta 2030 ta gudana cikin gaskiya da adalci.
