<span></span>
Dakarun Rundunar Operation HADIN KAI sun daƙile yinƙurin sace ɗalibai da wasu mayaƙan ISWAP suka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta ’Yan Mata (FGGC) da ke Monguno a Jihar Borno, tare da ceto ɗalibai 46.
Muƙaddashin kakakin rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Lahadi.
Ya ce maharan sun shiga makarantar da taimakon wasu da ake zargin masu ba su bayanai ne.
Ya ce jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki tare da buɗe wa maharan wuta.
Hakazalika, ya ce Rundunar Bayar da Agajin Gaggawa ta isa wajen domin kara ƙafara tsaro.
Hakan ya tilasta wa maharan tserewa ba tare da sun yi garkuwa da ko ɗalibai guda ɗaya ba.
Ko da yake wasu gine-ginen makarantar sun lalace sakamakon musayar wuta da aka yi da maharan.
Sojoji tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda sun kwashe ɗalibai 46 zuwa Barikin Kinnasara da ke Monguno, inda aka duba lafiyarsu.
Rundunar ta tabbatar da cewa dukkanin ɗaliban da aka ceto suna cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai, wasu ɗalibai sun rasa rayukansu bayan harsasai sun same su yayin musayar wutar.
Rundunar ta jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, tana mai cewa ana ci gaba da ƙoƙarin gano tare da cafke waɗanda ake zargin sun taimaka wa maharan.
Rundunar Operation HADIN KAI, ta ce za ta ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda tare da kare makarantu da sauran muhimman cibiyoyi a yankin Arewa maso Gabas.
