Yadda Ake Faten Dankalin Turawa Da Kaza
Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake Faten Dankalin Turawa.
Faten dankalin turawa da kaza abinci ne mai saukin hadawa, mai dadin ci kuma mai gina jiki.
Abubuwan da ake bukata:
Dankalin turawa matsakaici guda 8–10, Kaza (hanta) rabin kilo, Albasa guda 2, Tumatir manya guda 3, Tattasai guda 4, Attarugu guda 2 (gwargwadon bukata), Koren Tattasai guda 2, Koren albasa kadan, Mai, Kori, Tayim, Tafarnuwa da citta (an nika), Magi, Gishiri, Kayan kamshi.
Yadda ake hadawa:
Da farko a bare dankalin turawa, a wanke shi sannan a yanka shi kanana. A dan soya shi ko kuma a dafa shi kadan, sannan a ajiye a gefe.
A wanke kaza sosai, a yanka ta kanana, sannan a dafa ta tare da albasa, tafarnuwa, citta, magi da dan gishiri har sai ta yi laushi.
A markada tumatir, tattasai da attarugu. A dora tukunya a kan wuta, a zuba mai, sannan a soya albasa tadanyi ja. Bayan haka a zuba markadadden kayan miya, a bar su su soyu sosai.
A kara kori, tayim, magi da sauran kayan kamshi, sannan a zuba kazar da aka dafa tare da dan ruwanta. Bayan mintuna kadan, a zuba dankalin turawar da aka tanada, a juya a hankali domin kayan miya su hadu da shi.
A karshe, a yayyafa yankakken koren tattasai da koren albasa, sannan a sauke daga wuta.
Ana iya kara karas da koren wake domin karin armashi da gina jiki.
