Sabon Rahoton Bankin Duniya Ya Yaba Da Yadda Tattalin Arzkin Nijeriya Ke Bunkasa
Bankin Duniya ya kara nanata kalamansa na cewa, Nijeriya na kasa da karfin tattalin arzikin a 2027.
Hakan ya sanya kasar a cikin rukunin kasashen da ke karfin tattalin arzikin da ya kai kaso na dala 1,176 zuwa dala 4,635.
Bankin ya bayyana haka ne, a cikin rahotonsa na kwana-kwanan, na samun kudaden shigar kasar, wanda ya yi amfan da alkaluman tattalin arziki, na 2025.
A cewar Bankin, ya fitar da bayanin ne, ta hanyar dogara kan musayar kudade da kuma yadda kudade ke hawa suna sauka, inda aka kwatanta, da na sauran kasashe.
A cewar rahoton Bankin, Nijeriya ta shiga cikin sahun kasashe kamar su, Ghana, Kenya, Côte d’Iboire, Senegal, Kamaru, Angola da Zambia, da ke da kasa da tattalin arzikin a Afirka, inda suma wadannan kasashen, ke da sama da kaso 14,375.
Bankin ya kara da cewa, kasashen Afirka ta Kudu, Botswana, Mauritius, Gabon, Cabo Berde da Ekuatorial Guinea, sun ci gaba da kasancewa, a sama da ke da karfin tattalin arzki.
A cewar Bankin, Nijeriya ta ci gaba da kasancewa, mai kasa da karfin tattalin arzikin tun a 2010.
Sai dai, gwamnatin tarayya, na ci gaba da wanzar da tsarin tafiyar da kudaden kasar, musamman ta hanyar kirkiro da sauye-sauye, ga fannin tattalin arzikin kasar, daidaia bangaren zuba jari da kara karfafa fitar da kaya zuwa ketare.
