<span></span>
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci gwamnonin jihohin Arewa Maso Gabas da su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci da kuma ’yan bindiga, inda ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙarin haɗin kai domin inganta tsaro a yankin.
Da yake jawabi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis, Tinubu ya shaida wa shugabannin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe cewa Najeriya za ta iya shawo kan ƙalubalen da ke gabanta idan aka haɗa kai.
Shugaban ya kuma ce tattalin arziƙin ƙasar ya fara bunƙasa, yana mai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki domin inganta rayuwar al’umma.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa, ciki har da titin Akwanga–Bauchi–Gombe–Biu–Maiduguri.
Hakazalika, ya bayyana cewa gwamnati na cika alƙawuran da ta ɗauka na inganta ababen more rayuwa a yankin Arewa Maso Gabas.
Ya kuma ce gwamnatinsa na biyan bashin fansho da aka gada daga gwamnatocin baya, tare da jaddada aniyar gyara matsalolin da suka gabata ba tare da ƙorafi ba.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ya jagoranci tawagar, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa zaɓen Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027.
Zulum, ya kuma yaba da ayyukan gwamnatin Tinubu a fannonin gina hanyoyi, ilimi, noma, samar da ayyukan yi da kuma tallafawa mutanen da rikici ya raba da muhallansu.
Ya kuma yi alƙawarin cewa yankin Arewa Maso Gabas zai mara wa Tinubu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC baya a zaɓen shekarar 2027.
