Baya Ga “Sanyi Irin Na Sin”, Akwai Wasu Abubuwa Da Yawa Da Masu Yawon Bude Ido Na Turai Ke Sha’awa Kan Kasar
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a jiya Juma’a, inda mataimakin ministan tsaron jama’a ya fitar da wasu kididdiga. A farkon rabin shekarar nan, yawan bakin da suka shigo kasar Sin ya kai 22,914,000, ciki kuwa wadanda suka shigo ba tare da biza ba sun kai 17,815,000, wato adadin da ya karu da kashi 20.4 bisa dari da kuma kashi 30.6 bisa dari bi-da-bi, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Abin lura a nan shi ne, tun da aka shiga lokacin zafi, adadin baki masu yawon shakatawa daga kasashen waje ya yi ta karuwa, musamman ma wadanda suka fito daga Turai.Me ya ja hankalin masu yawon bude ido na Turai suka yi ta tururuwa zuwa kasar Sin? Dalilin haka kai tsaye shi ne suna da bukata matuka ta gudun zafi.
A wannan lokacin zafi na bana, wata babbar guguwar zafi ta mamaye Turai, lamarin da ya sa aka yi ta odar na’urorin sanyaya daki kirar kasar Sin sosai a wurin. Domin gudun zafin yanayin da suke ciki, al’ummar Turai sun fi sha’awar zuwa kasar Sin domin su mori “yancin jin sanyin na’urar sanyaya daki”, saboda akwai na’urorin sanyaya daki a manyan kantuna, otal-otal, tashoshin jirgin karkashin kasa da sauran wuraren jama’a a kasar Sin, inda ta hakan ake iya jin dadi sosai. Bugu da kari, kasar Sin kasa ce mai fadi da yawan albarkatu, wuraren halittu na gudun zafi masu dama da take da su, na iya bai wa masu yawon bude ido na Turai zabuka daban-daban na “jin dadin sanyi”.
Har wa yau, “Tafi kasar Sin nan take” abu ne mai sauki. A halin yanzu, kasar Sin tana aiwatar da manufar shigowa kasar ba tare da biza ba daga bangarenta ga masu dauke da fasfo na gama-gari daga kasashen Turai 35, kuma wadanda suka cika sharuddan za su iya zama har tsawon kwanaki 30 a kasar.
Daga abin da ke jan hankulan baki masu yawon shakatawa daga Turai su zo kasar Sin kuma, akwai kuma nasarori da kasar ta samu kan gudanar da harkokinta.
Jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta yi nuni da cewa, a dandalolin sada zumunta na kasashen waje, kasar Sin ta zama kasa mai dadin zuwa.Haka nan, a wannan lokacin zafi na bana, yayin da wasu ’yan siyasar Turai suka sake yayata batun kariyar cinikayya, baki daga Turai da suka zo kasar Sin domin yawon bude ido, sun tabbatar da wata gaskiya a bayyane, wato Sin da Turai abokan tarayya ne a maimakon abokan gaba. (Bilkisu Xin)
