Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Fara Aiwatar Da Shirin Inshorar Lafiya Ga Jaruman Kannywood
Shirin nan da gwamnatin Jihar Kano ta fito da shi na inganta walwala da jin dadin masu harkar finafinai a masana’antar Kannywood ta hanyar basu inshorar lafiya kyauta ya fara aiki, mujallar Fim ta ruwaito cewa za a fara aiwatar da shirin ne ta hanyar Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (Kano State Contributory Healthcare Management Agency (KSCHMA).
Hakan ya fito ne bayan wata ganawa ta musamman da aka gudanar a Kano tsakanin kwamitin KSCHMA da kuma Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano, taron ya mayar da hankali ne kan hanyoyin tabbatar da cewa membobin Kannywood sun samu ingantacciyar kulawar lafiya ta hanyar tsarin inshorar lafiya.
A yayin taron, an jaddada cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da shigar da membobin Kannywood cikin shirin ‘Bulnerable Group Health Care Programme’, wanda shiri ne na hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da hukumar KSCHMA wanda Hajiya Rahila Aliyu Mukhtar ke jagoranta, karkashin wannan tsari za a yi wa ‘yan Kannywood rajistar inshorar lafiya ba tare da sun biya ko sisi ba.
Haka kuma shirin zai bai wa kowane dan Kannywood da ya yi rajista damar samun kulawar lafiya tare da mata guda daya da yara hudu, a matakin farko, a yayin rajistar, kowane mutum zai zabi asibitin da yake son ya rika zuwa domin samun kulawa da magani, bugu da kari bayan kammala rajistar, KSCHMA za ta rika shiryawa da duba lafiyar ‘yan Kannywood kyauta duk bayan wata shida.
Haka kuma za a rika zaben wasu daga cikin yan fim domin gudanar da cikakken gwajin lafiya, da nufin gano cututtuka tun kafin su tsananta, dangane da wannan gagarumin tallafi, kwamitin Kannywood Abba Care ya bayyana aniyar sa ta neman ganawa da Gwamna domin mika masa godiya ta musamman bisa wannan karamci da kulawar da gwamnatin jihar ta nuna wa masana’antar.
