<span></span>
Kuɗin sufurin ababen hawa ya yi tashin gwauron zabi a sassa daban-daban na ƙasar nan, sakamakon tashin farashin man fetur zuwa Naira 1,400 kan kowace lita.
Wannan matsi ya biyo bayan tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, sakamakon rikicin da ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran.
Wannan al’amari ya janyo tashin farashin tataccen man fetur a faɗin Najeriya.
Hakazalika, Matatar Dangote ta mayar da farashin sayar da mai ga dillalai kan Naira 1,215 kan kowace lita, bayan dawo da sahar da man a Naira.
Sakamakon haka, gidajen mai da dama sun sauya farashinsu, inda a yanzu suke sayar da lita ɗaya tsakanin Naira 1,260 zuwa Naira 1,400, ya danganta da yanki.
Fasinjoji da dama sun bayyana cewa a yanzu suna kashe kuɗaɗen da suka ninka na baya wajen zirga-zirga.
A ɗaya ɓangaren kuma, direbobin motocin haya, sun bayyana cewa ba su da wani zaɓi da ya wuce na ƙara kuɗin mota domin daidaita lamarin da tsadar man fetur.
Mazauna birane da dama suna fargabar cewa ƙara kuɗin sufuri zai haifar da tashin farashin kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi, lamarin da zai sake jefa rayuwar talakawa cikin mawuyacin hali.
A Birnin Tarayya, Abuja, wasu fasinjoji sun tabbatar da cewa kuɗin mota ya ƙaru da kashi 20 zuwa 40 cikin ɗari a baya-bayan nan.
Sai dai direbobi sun ɗora alhakin hakan kacokan a kan tsadar man fetur.
A Jihohin Kaduna, Adamawa da Borno ma, farashin man fetur ya tashi, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa na haya ƙara wa fasinjoji kuɗi.
Sai dai kuma, a birane irin su Kano da Ibadan, kuɗin ababen hawa bai ƙaru sosai ba duk da tashin farashin man fetur ɗin.
Wasu daga cikin dillalan man fetur sun bayyana cewa wannan canji na farashi akai-akai yana kawo musu cikas wajen gudanar da kasuwancinsu.
Haka su ma direbobin motocin haya sun koka kan cewa suna fuskantar ƙalubale wajen samun kuɗaɗen gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Masana a fannin makamashi sun bayyana cewa wannan hauhawar farashin ta faru ne sakamakon barin kasuwar man fetur ta ci gashin kanta, inda farashinsa ya dogara da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma farashin canjin kuɗi.
Sun yi gargaɗin cewa farashin zai iya ci gaba da hauhawa matuƙar farashin ɗanyen mai bai sauka ba a kasuwannin duniya.
Hakan ya sa ’yan Najeriya da dama yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta ɗaukar matakai domin daidaita farashin man fetur tare da rage raɗaɗin tsadar rayuwa.
Sun nuna damuwa kan cewa ƙarin na iya ƙara jefa magidanta da ƙananan ’yan kasuwa cikin tsananin matsin tattalin arziƙi.
