NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci
Ajaero, ya ce kungiyar ba za ta amince da sake duba albashin ma’aikata ba tare da an kara kudaden fansho ga masu ritaya ba. Ya kuma bayyana cewa kungiyar kwadagon za ta yi fafutukar samar da Mafi Karancin Kudin Fansho na Kasa.
Ajaero ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da Gidan Tarihi Na ‘Yan Fansho Na Kwamared Godwin Abumisi da Babban Zauren Taruka mai Inganci da ke Abuja.
Ya ce hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa sun sa albashin mafi kankanta da kudaden fansho na yanzu ba su isa ba, lamarin da ya jefa ma’aikata da masu ritaya cikin mawuyacin hali.
“A halin yanzu muna shirin gudanar da babbar fafutuka ta kasa domin a yi cikakkiyar bita kan albashin mafi kankanta na kasa,” in ji Ajaero.
“Amma ba zai kara zama abin karbuwa ba a tattauna jin dadin ma’aikata ba tare da an tattauna jin dadin wadanda suka yi ritaya bayan sun shafe shekaru suna yi wa kasa hidima ba.”
Ya ce NLC za ta yi yakin neman samar da sabon albashin mafi kankanta tare da kafa Mafi Karancin Kudin Fansho na Kasa.
A cewarsa, “Babban rashin adalci ne a tarihi a tilasta wa maza da mata da suka sadaukar da kuruciyarsu da shekarun karfinsu wajen yi wa wannan kasa hidima su rayu a kasa da matakin talauci bayan sun yi ritaya.”
Ajaero ya ce ci gaba da tashin farashin abinci, kula da lafiya da sufuri ya sa rayuwa ta kara tsananta ga masu karbar fansho.
“Ba za mu ci gaba da barin tsofaffin ‘yan kasarmu suna rayuwa da kudin fansho da suka zama tamkar albashin talauci ba. Duk wanda ya yi ritaya ya cancanci rayuwa cikin mutunci bayan shekaru da dama na hidima ta gaskiya ga kasa,” in ji shi.
Shugaban NLC ya bukaci masu ritaya su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai tare da shirya wa fafutukar da ke tafe, yana mai cewa sabon ginin Legacy House zai zama cibiyar hadin kai da shirya gwagwarmaya.
Haka kuma, Ajaero ya yi kira da a gaggauta biyan dukkan bashin kudaden fansho da ake bin masu ritaya, tare da aiwatar da tsarin fansho da zai tabbatar da cewa kowane mai ritaya yana rayuwa cikin walwala da mutunci.
“Tare za mu ci gaba da gwagwarmaya har sai kowane ma’aikaci da mai karbar fansho a Nijeriya ya samu adalci, girmamawa da walwalar da ta cancanta,” in ji shi.
