Rashin jin shawara: Akwai wasu mutane da ba sa karɓar nasiha ko gyara, duk yadda aka yi...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Sin ta sha alwashin karfafa musaya da kasar Sweden a dukkanin fannoni, da amfani da fifikonsu, da ingiza hadin gwiwar cimma moriyar juna, da bunkasa dangantakarsu bisa turba mai nagarta, daidaito da dorewa. Wang Yi, ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin da yake zantawa da firaministan Sweden Ulf Kristersson a birnin Stockholm. Wang, ya kuma ce alakar Sin da Sweden ta gamu da wasu wahalhalu a shekarun baya-bayan nan, kuma wani abu mai matukar muhimmaci ga sassan biyu shi ne karfafa shawarwari, da bunkasa fahimtar juna, da gina aminci, tare da kara fahimtar juna yadda ya kamata. Kazalika, karuwar ci gaban kasar Sin zai amfani duniya baki daya, tare da samar da sabbin damammaki ga dukkanin kasashen duniya, ciki har da Sweden. Wang ya kuma yi fatan Sweden za ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata alakar Sin da Turai. A nasa bangare kuwa, mista Kristersson ya ce gwamnatin Sweden na nacewa manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma a shirye take ta karfafa tattaunawa, da fadada amincewa juna, da ingiza hadin gwiwar cimma moriya mai kyakkyawar makoma a dukkanin fannoni tare da Sin. Ya ce Sweden na goyon bayan Turai da Sin a fannin karfafa shawarwari, da inganta shawo kan sabanin dake tsakaninsu. (Saminu Alhassan)
Gwamnatin Jihar Gombe, ta hannun Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Wasanni, ta gudanar da...
Gwamnatin Jihar Gombe, ta hannun Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Wasanni, ta gudanar da...
Wasu alƙaluman hukumar Lafiya ta duniya WHO sun bayyana cewa mutum fiye da dubu 1,300 ne tsananin...
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim El-Hassan Kwami, kuma Sarkin Sudan...
Muaaddashin Shugaban Hukumar da ake shirin kafa ta National Institute for Public Health and Infectious Diseases (NIPHID)...
’Ya’yan Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, sun rasu a wani mummunan...
A kwanakin baya ne, matashin furodusan fina-finai a masana’antar Kannywood, Sultan Abdulrazak Dorayi ya bayyana kammala gina...
Ƙungiyar Real Madrid ta sanar da ɗaukar ɗan wasan baya na ƙasar Netherlands, Denzel...
