<span></span>
Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara rabon gonaki ga manoma 74 na al’ummar Jobi da ke ƙaramar Hukumar Maigatari, a wani mataki na kawo ƙarshen rikicin filayen noma da ya daɗe a tsakanin ƙauyen Jobi na Najeriya da ƙauyen Kyalli da ke Jamhuriyar Nijar.
An gudanar da bikin ƙaddamar da rabon gonakin ne a Dajin Dan-Makama, inda aka fara aiwatar da shawarwarin Kwamitin Iyakokin Jihar Jigawa, bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma Hukumar Kula da Iyakokin Najeriya (Hukumar kan iyakokin kasa-NBC).
Da take jawabi a madadin Darakta Janar na Hukumar, Surɓeyor Adamu Adaji Mataimakiyar Darakta mai kula da Iyakokin Ƙasa da Ƙasa, Hajiya Yahanasu Aliyu, ta bayyana cewa rabon a madadin gonakin wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan kan iyaka.
Ta ce, hukumar ta taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin cikin lumana, bisa nauyin da doka ta ɗora mata na inganta zaman lafiya da kyakkyawar alaƙa tsakanin al’ummomin da ke kan iyakokin ƙasa.
A cewarta, bayan cimma yarjejeniya cewa manoman Jobi za su daina noma a filayen da ke ƙarƙashin ƙauyen Kyalli a Jamhuriyar Nijar, hukumar ta ba da shawarar a samar musu fili a madadin gonaki.
Ta yaba wa Gwamnatin Jigawa bisa amincewa da wannan shawara tare da ware filin da ya dace domin amfanin manoman da abin ya shafa, tana mai cewa hakan ya nuna jajircewar gwamnati wajen kare hanyoyin samun abinci da kuɗaɗen shiga na al’umma tare da bunƙasa zaman lafiya tsakanin maƙwabtan kan iyaka.
Hukumar ta kuma yaba wa Gwamna Malam Umar Namadi bisa abin da ta bayyana a matsayin shugabanci nagari da saurin ɗaukar mataki, tare da ƙarfafa gwiwar waɗanda suka amfana da su rungumi wannan dama cikin ruhin zaman lafiya, mutunta juna da kyakkyawar maƙwabtaka.
Da yake gabatar da rahoton Kwamitin Iyakokin Jihar Jigawa, Mataimakin Gwamnan Jihar kuma Shugaban Kwamitin ya bayyana cewa rikicin ya shafi filayen noma da al’ummar Jobi ke iƙirarin mallaka a ƙaramar Hukumar Maigatari da kuma al’ummar Kyalli da ke Sashen Dungass na Yankin Zinder a Jamhuriyar Nijar.
Ya ce, rikicin na iya jefa kyakkyawar alaƙar da ta daɗe tsakanin al’ummomin biyu cikin barazana idan ba a warware shi cikin gaggawa ba.
Ya bayyana cewa, bisa umarnin Gwamna Umar Namadi, kwamitin ya gudanar da tattaunawa da sarakunan gargajiya, hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da jami’an Hukumar Kula da Iyakokin Najeriya kafin gabatar da shawarwarin warware rikicin.
