<span></span>
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan yaƙi da ta’addanci da kuma magance matsalolin tsaro a Najeriya.
A cikin wata wasiƙa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Laraba, Trump ya yaba da ƙoƙarin Tinubu na magance matsalolin tsaro, musamman hare-haren da ke shafar Kiristoci.
Ya ce Amurka na alfahari da tsayawa tare da Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci, kuma za ta ci gaba da tallafa wa ƙasar domin ta zama mafi aminci da ci gaba.
Trump, ya bayyana cewa ƙasashen biyu sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu ta fuskar tsaro.
Yarjejeniyar wadda ta haɗa da musayar bayanan sirri, horas da sojoji da kuma gudanar da ayyukan haɗin gwiwa kan ƙungiyoyin ta’addanci.
Ya kuma ce Amurka ta tura dakarun soji na musamman domin horas da sojojin Najeriya kan amfani da bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da ta’addanci.
Trump, ya ƙara da cewa yana fatan ci gaba da tattaunawa da Shugaba Tinubu domin ƙara bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka.
