<span></span>
Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, sun ƙone motoci huɗu, ciki har da babbar mota ɗauke da kayayyakin ‘yan kasuwa na miliyoyin Naira, a wani hari da suka kai garin Geidam da ke Ƙaramar Hukumar Geidam a Jihar Yobe.
Rahotanni sun nuna cewar harin ya auku ne da misalin ƙarfe 4:30 na safiyar Juma’a, lokacin da yawancin mazauna garin ke barci.
Mazauna garin sun ce maharan sun fara kai hari sakatariyar Ƙaramar Hukumar, inda suka ƙone mota ƙirar Toyota Hilux da kuma wata motar bas mallakin Ƙaramar Hukumar.
Bayan sun bar sakatariyar, maharan sun ci karo da manyan motoci biyu.
Ɗaya daga cikinsu na ɗauke da kayayyakin ‘yan kasuwa da suka zo cin kasuwar mako-mako ta Geidam.
Wata majiya ta ce ‘yan kasuwar sun loda kayansu tun cikin dare, suna jiran gari ya waye kafin su tafi.
Sai dai maharan suka ƙone motar tare da dukkanin kayan da ke cikinta.
Hakazalika, kuma ƙone wata mota da aka ajiye a cikin kasuwar.
Wani mazaunin garin ya ce maharan sun shiga garin ne a ƙafa bayan sun bar baburansu a wajen gari
Rahotanni sun ce ba a samu asarar rai ko jikkata ba a harin.
Mazauna yankin sun yi kira ga Gwamnatin Tarayyar, gwamnatin Jihar Yobe da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen samar da isasshen tsaro da kayan aikin da jami’an tsaro ke buƙata domin daƙile irin waɗannan hare-hare.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar harin.
Sai dai ya ce yankin Geidam na ƙarƙashin kulawar sojoji, saboda haka ya buƙaci a tuntuɓi rundunar sojin domin ƙarin bayani.
Ƙoƙarin jin ta bakin muƙaddashin kakakin Rundunar Haɗin Kai ta Arewa maso Gabas, Laftanar Ibrahim Kaita Bishir, bai yi nasara ba.
