<span></span>
Rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK) ta ceto mutum shida da ’yan ta’adda suka sace a Jihar Borno.
Waɗanda aka ceton sun haɗa da manya huɗu da jarirai biyu.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar.
Ya ce an ceto mutanen ne bayan bincike da hare-haren da sojoji suka gudanar bisa bayanan sirri a yankin Talakawa da ke Ƙaramar Hukumar Chibok.
Sanarwar ta ce an gano mutanen ne a yankin Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba.
Yanzu haka an kai su waje mai tsaro, inda ake kula da lafiyarsu tare da ba su kayan agaji kafin a haɗa su da iyalansu.
Rundunar ta ce wannan nasara ta nuna irin ƙoƙarin da sojoji ke yi tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Borno da sauran hukumomin tsaro wajen ceto mutanen da aka sace.
A yayin aikin, sojojin sun kuma ƙwato harsasai 50 na bindigar PKT da ’yan ta’adda suka bari yayin da suke tserewa.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ceto da kuma matsa wa ‘yan ta’adda lamba har sai an kuɓutar da duk sauran waɗanda ke hannunsu.
Ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri kan duk wani abu da suke zargi, tare da guje wa yaɗa labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
