Sin Da Rasha Za Su Gudanar Da Atisayen Sojojin Ruwa Da Sintiri Na Hadin Gwiwa
Rundunonin sojojin ruwan kasar Sin da na Rasha sun shirya gudanar da atisayen soji, da sintiri na hadin gwiwa a sassan ruwa da sararin sama, nan gaba cikin wannan wata na Yuli, a kusa da birnin Qingdao dake lardin Shandong na gabashin kasar Sin.
Wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar Sin ta fitar a Lahadin nan, ta tabbatar da shirin gudanar da atisayen mai lakabin “Joint Sea-2026”.
Ta kuma ce bayansa, wasu dakarun kasashen biyu za su aiwatar da sintiri a wasu yankuna masu nasaba dake kan tekun Fasifik.Ma’aikatar ta kuma ce atisayen, wani bangare ne na shirin hadin gwiwa na shekara-shekara tsakanin dakarun sojin kasashen biyu, wanda ke da nufin hadin gwiwa don tunkarar tarin kalubalen tsaro, da tabbatar da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. (Saminu Alhassan)
