<span></span>
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙarfafa yaƙi da matsalar tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani, inganta tattara bayanan sirri da kuma ƙara wa rundunar sojojin ƙasar ƙarfi.
Tinubu, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilta a bikin Ranar Sojin Najeriya ta 2026 da aka gudanar a Fatakwal, ya ce gwamnati na ci gaba da zuba jari wajen samar da sabbin kayan aikin soja da kuma horar da jami’ai domin su tunkari sabbin barazanar tsaro.
Ya ce gwamnati za ta kuma bunƙasa bincike da ƙera kayan aikin soja a cikin gida ta hanyar ƙarfafa Kamfanin Masana’antun Tsaro na Najeriya (DICON), domin rage dogaro da kayan aikin soji da ake shigowa da su daga ƙetare.
A cewarsa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar wa jami’an tsaro duk abin da suke buƙata domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Tinubu ya kuma yaba da jarumtar dakarun sojin Najeriya wajen kare haɗin kan ƙasa da kuma yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara inganta walwala da jin daɗin jami’an soji domin ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Shi kuwa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare martabar ƙasa da rayuka da dukiyoyin al’umma duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.
