<span></span>
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta ninka mafi ƙarancin albashin sojojin Najeriya na kowane wata daga Naira dubu 49 zuwa N100,000, a matsayin wani sabon yunƙuri na inganta jin daɗin dakarun ƙasar da kuma ƙarfafa musu gwiwa.
Ministan Tsaro, Christopher Musa ne ya bayyana wannan sabon nazari kan albashi yayin wata hira da ya yi da tashar talabijin na News Central.
Ya bayyana wannan ci gaba a matsayin ɗaya daga cikin sauye-sauyen inganta jin daɗin rayuwa da gwamnati mai ci yanzu ta ɓullo da su domin jami’an tsaro.
“Lokacin da aka fara, soja yana kar ɓar N49,000 ne a kowane wata. Mun yi iyakacin ƙoƙarinmu, yanzu yana kar ɓar N100,000,” in ji Ministan.
Shekaru da dama, damuwa game da ƙarancin albashi, rashin muhalli mai kyau, jinkirin biyansu alawus-alawus, da kuma tsadar rayuwa da ke raddadi, su ne suka mamaye muhawara kan jin daɗin dakarun soja.
Haka kuma, Musa ya ƙaryata zargin cewa, ana ba sojoji abinci maras kyau, inda ya bayyana jita-jitar da ke yawo a kafofin sada zumunta a matsayin abin yaudara.
Yayin da yake magana a kan wani bidiyo da ya yaɗu wanda ya shafi wani babban jami’in soja mai suna Justice Crack, ministan ya yi zargin cewa an canza fasalin bidiyon ne da gangan domin nuna bogi game da ingancin abincin da ake ba dakarun.
“Abincin sojan yana da kyau. Akwai nama; akwai komai a ciki. Amma ya gaya musu da su cire waɗancan abubuwan domin su nuna kamar babu su a ciki,” in ji shi.
Kalaman na Ministan na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da amfani da dabarun haɗaka na sauya fasalin jin daɗin ma’aikata, ƙara kuɗaɗen kashewa a fannin tsaro, da kuma ƙaddamar da sabbin ayyukan soja da nufin inganta karsashin dakarun da ke yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar.
