<span></span>
Bayan kwashe kwanaki sama da 50 da sace ɗalibai da malamai a Jihohin Oyo da Borno, har yanzu iyayen waɗanda abin ya shafa suna cikin fargaba da jiran tsammani, yayin da da dama daga cikinsu ke kukan cewa hukumomin tsaro ba su ba su bayanai kan halin da yaransu ke ciki ba.
A Jihar Oyo, idan za a tuna wasu ’yan bindiga ne suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai guda 46, har da shugaban makarantar sakandaren ‘Community High School’ da ke garin Ahoro-Esiele a Ƙaramar Hukumar Oriire, a ranar 15 ga watan Mayu.
Daga bisani, miyagun suka hallaka ɗaya daga cikin malaman mai suna Michael Oyedokun.
A wannan rana ne kuma, wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne, suka kai hari makarantun firamare da sakandare na Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno, inda suka yi garkuwa da ƙananan yara maza da mata sama da 40.
Lamarin ya jefa al’ummar ƙasar cikin fargaba, wanda hakan ya sa iyaye, ƙungiyoyin malamai, da na fararen hula suka yi kira gwamnati da ta tashi tsaye domin ceto ɗaliban da malaman.
Ministan tsaro ya bayyana dalilin jnkirin ceto ɗaliban Oyo
Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyan cewar fargabar yi wa ɗaliban da malaman kisan-gilla ne ya sa suka jinkirta kai samame maɓoyar maharan.
Ya ƙara da cewa, maharan suna amfani da rayuwar yaran da malaman ne a matsayin garkuwa domin tursasa wa hukumomi su saki wasu daga cikin manyan shugabanninsu da ke tsare.
“Suna neman hanyar matsa mana lamba ne saboda wasu jagororinsu suna hannunmu. Suna tsammanin riƙe waɗannan yara za ta tilasta mana sako musu mutanensu,” in ji Musa.
“A duk lokacin da muka yi yunƙurin ƙwato su da ƙarfin soji, sai su yi barazanar cewa muddin muka kusanci inda suke , za su kashe dukkanin yaran.”
Ministan ya yi kira da a tsaurara hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, inda ya bayyana cewa hakan ne kawai zai zama izna ga sauran masu shirin aikata laifin.
“Yana da matuƙar muhimmanci a samar da tsauraran dokoki da za su tsoratar da masu laifi. Dokokinmu na yanzu suna da sassauci da rauni, hakan yana bai wa miyagu damar cin karensu ba babbaka,” in ji shi.
A gefe guda kuma, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an yi nasarar cafke wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen maharan shirin sace yaran, bayan shafe makonni ana tattara bayanan sirri.
Wannan kame ya sanya masu garkuwar cikin mawuyacin hali tare da kawo tsaiko a tattaunawar da ake yi da su.
Iyayen ɗaliban Borno sun ce har yanzu ba su san halin da ’ya’yansu ke ciki ba
Yayin da hankalin ƙasa ya karkata kan abin da ke faruwa a Jihar Oyo, iyaye da dangin yaran da aka sace a Jihar Borno sun nuna takaicinsu kan rashin sanin halin da ‘ya’yansu ke ciki.
Iyayen yara 42 da aka sace daga makarantun Mussa a garin Askira/Uba, sun bayyana cewa gwamnati da hukumomin tsaro sun daina shiga lamarinsu, domin sun daina ba su bayani kan halin da ake ciki ba.
Saleh Buba, mahaifin yara biyu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, ya bayyana cewa iyaye da dama na rayuwa ne cikin baƙin ciki da zulumi.
“Har yanzu ba mu da masaniya kan ko yaranmu suna raye ko a’a, kuma babu wani jami’in gwamnati da ya zo wajenmu domin kwantar mana da hankali ko shaida mana halin da ake ciki,” in ji shi.
Wani mutum kuma ya bayyana cewa halin rashin ko-in-kuls da hukumomi suka nuna musu ya fi musu yi zafi sama da rashin sanin halin da yaran ke ciki.
“Babu wanda ya zo ya faɗa mana cewar ga inda yaran suke ko ga matakin da ake kai. Muna cikin duhu dunɗum,” in ji shi.
Wannan dalili ya sa daga baya iyaye da sauran mazauna garin fitowa zanga-zangar lumana domin tilasta wa gwamnati ƙarfafa gwiwa wajen ceto yaran.
Gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen ceto ɗaliban
Biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da matsin lamba daga al’umma, Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Oyo, sun sanar da sabbin tsare-tsare domin inganta tsaro da hanzarta ceto waɗanda aka sace.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin jami’an tsaron gandun daji guda 1,000 a Jihar Oyo, tare da tura dakarun haɗin gwiwa na musamman don tallafawa aikin ceto ɗaliban jihar.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya fayyace cewa wannan karo za a gudanar da aikin ne cikin tsantsar ƙwarewa da dabaru.
“Wannan karon, aikin zai dogara ne kacokan kan bayanan sirri na zamani. Za a yi amfani da dabarun soji da kuma tattaunawa domin ganin yaran sun dawo gidajensu cikin ƙoshin lafiya,” in ji shi.
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, shi ma ya ziyarci yankunan da abin ya shafa domin jajantawa da kuma bai wa iyayen ɗaliban tabbacin cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an ceto yaran.
Daga baya gwamnan ya bayyana cewa bayanan sirri sun nuna cewa ana tsare da yaran ne a cikin dajin ‘Old Oyo National Park’, dajin da ke da duwatsu da sarƙaƙiya wanda hakan ke zame wa dakarun soji babban ƙalubale
Haka kuma, Gwamna Makinde ya tabbatar da rasuwar wani babban jami’in soji yayin fafatawa da maharan.
“Mun rasa jaruman jami’ai ciki har da sojoji. Ina tabbatar muku da cewa wani Laftanar na rundunar sojan ƙasa ya riga mu gidan gaskiya kwanaki biyu da suka gabata,” in ji gwamnan.
Bayan faruwar hakan, gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita ta tsawon lokaci a Ƙananan Hukumomi 10 da ke kusa da dajin domin tsaurara matakai.
Masana sun yi kira da a yi amfani da fasaha da bayanan sirri
Masana harkokin tsaro sun buƙaci gwamnati da ta sauya salo ta hanyar amfani fasahohin zamani da kuma bayanan sirri domin kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane da ta’addanci baki ɗaya.
Wani masani a fannin tsaro, Ridwan Aleshinloye, ya bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta dogara da jirage marasa matuƙa, kyamarorin sirri, da kuma ƙirƙirarriyar fasaha (AI) wajen bankaɗo maɓoyar miyagu.
“A halin yanzu, muna buƙatar dogaro da ƙarfin mutane da kashi 40 kacal, yayin da za mu zuba kashi 60 na ƙarfinmu a kan kimiyya da fasaha. Wannan ita ce hanya guda ta gano maɓoyar miyagu ba tare da jefa rayukan mutanen da ke hannunsu cikin hatsari ba,” in ji shi.
Shi ma a nasa ra’ayin, Manjo Janar Umar I. Mohammed (mai ritaya), ya amince cewa aikin ceto a daji yana da matuƙar hatsari, amma ya jaddada cewa tsari da ƙwarewa ne kaɗai za su iya sa a dawo da yaran cikin nasara.
Ya buƙaci rundunonin tsaro da su auna girman hatsarin da ke tattare da aikin ceto ɗaliban, kafin fara kai samame.
Yayin da aka kwashe makonni sama da bakwai da sace ɗalibai da malaman, har yanzu iyayen yaran da malaman na fatan hukumomin tsaro su ceto su cikin aminci.
