<span></span>
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunan Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa don yin takararsa a zaɓen Shugaban ƙasa na shekarar 2027.
An dai ta yin jita-jitar cewa shugaban kasar na iya ajiye mataimakinsa na yanzu saboda wasu lissafin siyasa.
An kuma yi hasashen cewa rashin komawar Shettima na iya fuskantar barazana, musamman ganin yadda wasu masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyya mai mulki ta APC, har ma da na shiyyar Arewa maso Gabas, suka gaza amincewa da shi.
Waɗanda ke fafutukar ganin an canza abokin yin takarar sun kuma riƙa yayata cewa, shugaban ƙasar na iya maye gurbin Shettima da wani Kirista ɗan Arewa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Sai dai a ranar Juma’a, Ibrahim Masari, Mai Taimakawa Shugaban ƙasa na Musamman kan Al’amuran Siyasa, ya miƙa takardun tsayawa takara na Tinubu da Shettima ga shugabannin APC a otal ɗin Continental da ke Abuja.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Gwamnonin da suka haɗa da: Gwamnan Imo, Hope Uzodimma da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris da Gwamnan Kaduna, Uba Sani da Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri da Gwamnan Borno, Babagana Zulum.
Miƙa takardun ya tabbatar a hukumance da shawarar da Tinubu ya yanke na riƙe Shettima a matsayin abokin takararsa a babban zaɓen shekarar 2027.
