<span></span>
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da ƙara wa’adin karɓar jerin sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya domin babban zaɓen shekarar 2027.
Hukumar ta bayyana cewa wa’adin wanda aka tsara tun farko zai ƙare ne a ranar Asabar, 11 ga Yulin 2026, amma yanzu an tsawaita shi zuwa ƙarfe 12:00 na daren ranar Talata, 14 ga Yulin 2026.
A cewar INEC, an ɗauki matakin ne bayan buƙatar da Majalisar Ba da Shawara ta Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta gabatar a madadin wasu jam’iyyun siyasa.
Hukumar ta ce wasu jam’iyyun ba su samu damar kammala ɗora sunayen ’yan takararsu da sauran bayanan da ake buƙata a shafinta na yanar gizo ba kafin cikar wa’adin da aka bayar a baya.
INEC ta buƙaci jam’iyyun siyasa da abin ya shafa su yi amfani da ƙarin lokacin domin kammala dukkan matakan da suka rage cikin sabon wa’adin da aka tanada.
