<span></span>
Tawagar Ingila ta kai wasan dab da na ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 bayan ta doke Norway da ci 2-1 a wasan kwata-fainal da aka buga a Amurka.
Norway ce ta fara zura ƙwallo a minti na 36 ta hannun Andreas Schjelderup, kafin Jude Bellingham ya farke wa Ingila mintuna kaɗan kafin a tafi hutun rabin lokaci, wanda ya sa aka tafi hutu ana canjaras 1-1.
Bayan an kammala mintuna 90 babu ƙarin ƙwallo, aka tafi ƙarin lokaci.
A minti na 93 ne Jude Bellingham ya sake zura ƙwallo ta biyu, wadda ta tabbatar wa Ingila nasarar 2-1 da kuma tikitin zuwa wasan dab da na ƙarshe.
Da wannan sakamako, Ingila za ta kara da Argentina a wasan dab da na ƙarshe, bayan da Argentina ta doke Switzerland da ci 3-1 a ɗaya wasan kwata-fainal.
