<span></span>
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki shirin Gwamnatin Tarayya na ƙara kuɗin jarabawar WAEC da NECO zuwa Naira 50,000 daga shekarar 2027.
Ya yi gargaɗin cewa matakin na iya sa ɗalibai da dama gaza kammala karatunsu.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya ce ƙarin kuɗin ya zo ne a lokacin da iyaye da dama ke fama da tsadar rayuwa, musamman hauhawar farashin kayan abinci, sufuri, wutar lantarki da sauran buƙatun yau da kullum.
Ya bayyana cewa ilimi ya kamata ya kasance abu mai sauƙin samu ga kowane ɗan Najeriya.
Ya kuma yi gargaɗin cewa ƙarin kuɗin jarabawar na iya zame wa ɗalibai da iyaye, musamman ƙaramin ƙarfi da waɗanda ke fama da matsalar tattalin arziƙi matsala.
Atiku, ya ce Najeriya na fuskantar matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, don haka ya kamata manufofin gwamnati su rage matsalolin da ke hana yara samun ilimi, maimakon ƙara yawansu.
Ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta sake duba wannan mataki tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin samun kuɗin tafiyar da harkokin ilimi.
Ya kuma buƙaci gwamnati ta ƙara zuba jari a makarantu, inganta kayayyakin more rayuwa da tallafa wa ɗalibai.
