Xi Zai Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026, Inda Zai Gabatar Da Muhimmin Jawabi
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar a yau Litinin cewa, za a gudanar da babban taron manyan jami’a na duniya kan tafiyar da sha’anin fasahar AI a birnin Shanghai, daga ranar 17 zuwa 20 ga wata.
Jami’in ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron tare da gabatar da muhimmin jawabi. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
