<span></span>
Iyayen wata yarinya mai shekara biyar sun nemi a hukunta wani mutum da ake zargi da yi wa ’yarsu fyaɗe a yankin Anguwan Rogo da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Mahaifiyar yarinyar, Suwaiba Iliyasu, ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne bayan ’yarta ta dawo daga makaranta, inda ta bayyana cewa wani maƙwabcinsu ya kai ta wani ɗaki ya ci zarafinta bayan ya yaudare ta da kuɗin sayen gyaɗa.
A cewar mahaifiyar, bayan sun kai rahoto ofishin ’yan sanda, an kai yarinyar asibiti, inda binciken likita ya tabbatar da cewa an yi lalata da ita, sannan aka kama wanda ake zargi.
Sai dai iyalan sun yi zargin cewa a ofishin ’yan sanda na A Division an buƙaci su biya Naira 50,000 kafin a buɗe fayil ɗin shari’ar da ci gaba da bincike, kuɗin da suka ce ba su da su ba su da kamarsu.
Mahaifin yarinyar, Hayatu Muhammad, ya ce suna kira ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Filato da sauran hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an gudanar da bincike ba tare da wata tangarɗa domin tabbatar da an yi wa ’yarsu adalci.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Alabo Alfred, ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
