<span></span>
‘Yan Majalisar Wakilai sun ba da umarnin gudanar da bincike kan dukkan kadarorin da aka ƙwace a cikin gida ko waɗanda aka ƙwato aka dawo da su daga ƙetare tun bayan dawowar Najeriya kan mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999 zuwa yanzu.
Majalisar ta ce akwai damuwa kan rashin gaskiya da rashin kiyaye ka’idojin gudanarwa da kuma matsalolin adana bayanai.
Matakin ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Arochukwu/Ohafia ta Jihar Abia, Ibe Okwara Osonwa, ya gabatar.
Ƙudirin ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike da tantance dukkan kadarorin da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da hukumomin tsaro da ma’aikatu, da hukumomi da cibiyoyin gwamnati haɗe da hukumomin sa ido da kuma kotuna ke kula da su.
