<span>Birnin Kalaba na Kuros Riba</span>
Wata Babbar Kotu mai lamba ta 11 da ke Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, ta yanke wa wani mutum mai suna Apostle Ubong Bassey Etim hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan ta same shi da laifin kashe ’yarsa, Deborah Bassey, bisa zarginta da maita.
Mai shari’a Blessing Egwu ta ce kotu ta gamsu da hujjojin da aka gabatar a gabanta cewa wanda ake tuhuma ya kashe ’yarsa ba tare da wani sahihin dalili ba, illa zarginta da aikata maita.
Da yake zantawa da Aminiya bayan yanke hukuncin, shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Basic Rights Counsel Initiative (BRCI), Barista James Ibor, ya ce hukuncin ya nuna cewa kotu ba za ta lamunci irin wannan ɗabi’a ba.
“Kotu ta tabbatar da cewa zargin maita da ake yi wa Deborah ba shi da wani tushe. Duk da haka, mahaifinta ya ɗauki doka a hannunsa ya kashe ta. Wannan hukunci adalci ne ga wadda aka kashe da kuma al’umma baki ɗaya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa hukuncin zai zama izina ga duk wanda ke da niyyar ɗaukar doka a hannunsa saboda irin waɗannan zarge-zarge marasa tushe.
Barista Ibor ya kuma yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba kan yadda ta gudanar da bincike, ta cafke wanda ake zargin tare da gurfanar da shi a gaban kotu har aka samu nasarar tabbatar da laifinsa.
