<span></span>
Wani sabon jami’in rundunar tsaron gwamnatin Jihar Sakkwato ta Sokoto Marshal, Mustapha Namadeena, ya rasu kwana guda bayan ya halarci bikin yaye sabbin jami’an rundunar.
Marigayin na daga cikin sabbin jami’an da suka kammala ɗaukar horo, inda aka yaye su a wani biki da aka gudanar ranar Alhamis a Filin Wasanni na Giginya da ke Sakkwato.
Bayanai sun ce Namadeena ya rasu ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a.
Kafin shiga rundunar, marigayin ya kasance Shugaban Kafofin Sada Zumunta na Jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa.
Wani abokan aikinsa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Namadeena ya yi fama da rashin lafiya tun lokacin da suke karɓar horon, lamarin da ya sa aka ba shi izinin komawa gida domin neman magani.
A cewarsa, marigayin ya dawo sansanin horaswar ne a jajibirin bikin yaye sabbin jami’an, inda suka halarci bikin tare.
Shi ma wani abokin aikinsa ya ce rasuwar ta girgiza shi, ya ce a wuri guda suka tsaya tare a wajen bikin yaye su, inda kuma ya bayyana cewa marigayin mutumin kirki ne, mai tawali’u da ƙwazo.
Har zuwa yanzu dai Rundunar Sokoto Marshal ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
