Idan Aka Cire Bangaren Man Fetur Kannywood Ce Ta Fi Samar Da Aikin Yi Ga Matasa —Hamisu Iyantama
Daya daga cikin dattawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma mamallakin kamfanin shirya fina-finai na Iyantama Multimedia Alhaji Hamisu Lamido Iyantama a wata hira da yayi da Gidan Talabijin na Edpress, ya bayyana cewar a halin da ake ciki yanzu masana’antar Kannywood ce kan gaba a bangaren samar da ayyukan yi a tsakanin matasa idan aka cire bangaren harkar Man Fetur a Nijeriya.
Alhaji Hamisu wanda yace yana daga cikin wadanda suka fara samar da kamfanonin shirya fina-finai a Arewacin Nijeriya, ya fara harkar fim shekaru fiye da 30 baya, inda ya fito kuma ya shirya manyan fina-finai a masana’antar, wadanda tarihin masana’antar Kannywood ba zai taba cika ba tare dasu ba, duk da cewar ya shafe tsawon lokaci ba tare da an ganshi a cikin fim ba, jarumin ya ce har yanzu yanada rawar da zai taka a masana’antar ta Kannywood.
“Sau da yawa nikan samu kiraye-kiraye ta hanyoyi da dama a kan miyasa na daina fitowa a fina-finai, masoya sukan ce sun fi sha’awar irin rawar da nake takawa a cikin fim ba kamar yadda suke gani a mafi yawancin fina-finan wannan zamanin ba”, a baya-bayan nan da na fito a cikin wani shiri na kamfanin Maishadda sai mutane suka dinga yabawa da irin yadda na gabatar da aikina a cikin fim din in ji shi.
Ya ci gaba da cewa “A farkon lokacin da aka fara wannan harka ta wasan kwaikwayo a wancan lokacin, wadanda suka fara assasa harkar basu taba tunanin za a kawo lokacin da harkar za ta bunkasa kamar yadda take a halin yanzu ba”, a wancan lokacin babu wanda ya taba tunanin harkar wasan kwaikwayo za ta zama abin da ta zama yanzu, saboda a wancan lokacin duk da cewar kudade ake zubawa ana shirya fim, amma bamu saka a ranmu cewar muna bukatar samun wata gwaggwabar riba ba, mun fi mayar da hankali wajen nuna al’adu da addininmu ba kamar yanzu da zamani ya canza komai ba.
Ya ci gaba da cewar a wancan zamanin ana gasar shirya fina-finai a tsakanin furodososhi, amma kuma ana yi ne kawai domin kara karfafa gwuiwa da neman shawarwarin juna, “zan iya kallon fim din da wani kamfani ya shirya, idan naga wani abu da zan koya sai in koya domin in yi amfani dashi a nawa fim din da zan yi, kamar yadda wani shima zai kalli nawa fim din ya yi amfani da abin da ya kalla ya saka a nashi”.
Da yake amsa tambaya dangane da zargin rashin hadin kai da aka ce masana’antar na fama dashi, Hamisu ya ce “A duk inda aka samu yawaitar mutane dole ne sai an samu banbance-banbancen ra’ayi wanda zai janyo ana samun sabani da ba a rasa ba, yanzu idan ka lura a duk fadin Nijeriya idan ka cire bangaren harkar Man Fetur babu wata masana’antar da ke samar da aikin yi kamar masana’antar shirya fina-finai, to kaga kenan akwai tarin al’umma da ke cikinta, wadanda ke da mabanbantan ra’ayoyi na kashin kansu”.
Daga karshe Alhaji Hamisu Lamido Iyantama ya bukaci masu shirya fina-finai a halin yanzu da su tabbatar suna tsare duk wasu dokoki da gwamnatin tarayya ta gindayawa harkar (Fim Act), inda ya ce ta wannan hanyar kadai ne za a ci gaba da samar da ingantattun fina-finai da za su yi daidai da bukatar masu kallo da kuma tsare hakkokinsu, a bangare daya kuma a kare martabar masana’antar ta Kannywood.
