<span>Murtala Sule Garo</span>
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da sake zaɓen mataimakinsa, Murtala Sule Garo, a matsayin abokin takararsa a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.
Sanarwar ta fito ne yayin wata ganawa ta dabarun siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnatin tarayya daga Jihar Kano a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano da ke Abuja.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin, Gwamna Yusuf ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa la’akari da biyayya, jajircewa da gudunmawar da Garo ya bayar tun bayan da zamansa mataimakin gwamna.
Ya bayyana gamsuwarsa da irin kyakkyawar alaƙar aiki da ke tsakaninsu, yana mai bayyana Garo a matsayin mutum mai ƙwarewa, jajircewa da riƙon amana wajen gudanar da ayyukansa.
“Ban taɓa yin nadamar zaɓen Garo a matsayin mataimakina ba, kuma ya tabbatar da cewa shi ne wanda ya dace da wannan muƙami. Ina tabbatar muku cewa ina da cikakkiyar amincewa da shi,” in ji Gwamna Yusuf.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Garo abokin aiki ne abin dogaro, wanda ya jaddada cewa yana bayar da gudunmawa da ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin wajen samar da ci gaba a faɗin Jihar Kano.
Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyarsu ta APC, masu riƙe da muƙaman siyasa da magoya baya da su ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗauri ɗaya da kuma ba gwamnatin goyon baya yayin da take ƙarfafa nasarorin da ta samu haɗi da shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko jam’iyyar APC ta amince da wannan zaɓi a hukumance ba, amma ta nuna cewa gwamnan na da niyyar ci gaba da tafiya tare da Garo a matsayin abokin takararsa a zaɓen gwamna na 2027.
