<span>Taswirar Jihar Katsina</span>
Ana fargabar cewa wasu yara biyu ’yan gida ɗaya — Muhammad Salisu mai shekara 12 da Abdurrahman Salisu mai shekara 7 — sun rasu bayan ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su a unguwar Janbago da ke Jihar Katsina.
Rahotanni sun ce yaran na kan hanyarsu ta dawowa gida daga makarantar Islamiyya ne lokacin da ruwan sama mai ƙarfi da iska ya haddasa ambaliya, wadda ta mamaye titunan unguwar.
Bayan dogon bincike da mazauna yankin suka yi, an gano gawarwakin yaran a wurare daban-daban.
Lamarin ya jefa al’ummar Janbago cikin jimami, inda jama’a suka yi tururuwa zuwa gidan iyayen yaran domin yi musu ta’aziyya.
Cikin alhini, mahaifinsu, Malam Salisu Arabi, ya ce wannan shi ne mafi muni cikin jarabobin da ya taɓa fuskanta.
“Sun fita kamar yadda sauran yara ke fita zuwa makarantar Islamiyya. Ban taɓa tunanin ruwan saman da muka gani zai raba ni da ’ya’yana biyu a rana guda ba.
“Ina roƙon Allah Ya jikansu Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu, sannan ina kira ga gwamnati ta ɗauki matakan da za su hana sake aukuwar irin wannan ibtila’i,” in ji shi.
Ita ma mahaifiyar yaran ta bayyana cewa rasuwar ’ya’yanta ta girgiza rayuwarta.
“Su ne farin cikina da fatana. Yau ambaliya ta raba ni da su. Ina roƙon gwamnati ta magance wannan matsala, domin ba na son wata uwa ta sake binne ’ya’yanta saboda ambaliya,” in ji ta.
Mazauna Janbago sun ce ana fama da ambaliya a yankin tsawon shekaru saboda rashin ingantattun magudanan ruwa.
Wani dattijo a unguwar ya bayyana cewa ruwan sama daga sassa daban-daban na Ƙaramar Hukumar Katsina kan gangaro zuwa Janbago, lamarin da ke haddasa zaizayar ƙasa, lalata hanyoyi da kuma jefa rayuka da dukiyoyi cikin haɗari.
Ya ce sun sha kai koke ga gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa, amma har yanzu ba a samar da wata mafita mai ɗorewa ba.
Shi ma Shugaban Ƙungiyar Cigaban Al’ummar Janbago, Malam Tajuddeen, ya ce matsalar ta shafe fiye da shekara goma tana addabar yankin.
“Ba wannan ne karo na farko da ambaliya ta auku ba, amma wannan shi ne mafi muni domin ta yi sanadin mutuwar yara biyu waɗanda ba su ji ba su gani ba. Duk shekara muna asarar dukiya, hanyoyi na lalacewa, kuma mutane na rayuwa cikin fargaba idan damina ta zo,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa al’ummar yankin sun sha rubuta wasiƙu suna neman gwamnatin jihar ta magance matsalar, amma har yanzu ba a samu mafita ba.
Ya yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, da ya gaggauta ɗaukar matakan gina magudanan ruwa da aiwatar da ayyukan kariya daga ambaliya domin kauce wa sake aukuwar irin wannan ibtila’i.
