<span></span>
An gano gawar wani ɗalibi mai matakin karatu na 200 a Jami’ar Tarayya da ke Kashere (FUK), Enoch Sunday Maisamari bayan kwanaki uku da ɓacewarsa.
An dai gano gawar ne a cikin wani tafkin kududdufin ruwa a ƙauyen Sabon Garin Yero, kusa da garin Kashere da ke ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.
Mamacin mai shekaru 28, ɗalibi ne a Sashen Ilimin Ƙwayoyin Halitta na Tsangayar Kimiyya ta jami’ar.
Rahotanni sun nuna cewa, ya ɓace tun ranar Lahadi, bayan ganinsa na ƙarshe a wani bikin kammala karatu da ɗaliban ajin ƙarshe suka shirya a jami’ar.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, ’yan sanda ne suka gano gawarsa da safiyar ranar Talata, kafin daga bisani su sanar da hukumomin jami’ar.
ɗaya daga cikin abokan karatunsa ne ya tabbatar da cewa, gawar ta Maisamari ce.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi ya ce an samu rahoton gano gawar da misalin ƙarfe 9:30 na safe ranar Laraba a cikin wani tafkin ruwan da yake tsaye baya gudu a Sabon Garin Yero da ke ƙaramar Hukumar Akko.
Ya ce, an kai gawar zuwa Babban Asibitin Kashere, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
A cewarsa, ba a samu wata alamar rauni ko tashin hankali a jikin mamacin ba, sai dai rundunar na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwarsa.
