<span></span>
Dakarun Rundunar Operation Haɗin Kai sun kama wani ɗan ƙasar Sudan da ake zargin yana da alaƙa da ta’addanci, tare da wata ‘yar ƙasar Ghana da ba ta da takardun zama a Najeriya, a yankin Askira/Uba da ke Jihar Borno.
A cewar rundunar, dakarun Bataliya ta 115 tare da Sashe na 4 na Operation HADIN KAI ne suka yi kamen yayin wani samame na leƙen asiri da suka gudanar da misalin ƙarfe 11:48 na ranar 19 ga Yuli.
Sojojin sun bayyana sunan mutumin da aka kama da Musa Fashir, mai shekara 32 ɗan ƙasar Sudan.
Sun ce bayanan farko da suka tattara sun nuna akwai yiwuwar yana da alaƙa da ƙungiyoyin ta’adda da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, lamarin da ke ƙara nuna damuwa kan yiwuwar shigar mayaƙan ƙasashen waje cikin ayyukan ta’addanci.
Haka kuma, dakarun sun kama Mary Florence, mai shekara 36, wadda ta bayyana wa masu bincike cewa ita ‘yar ƙasar Ghana ce kuma ba ta da takardun zama a Najeriya.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano dalilin zuwanta yankin tare da tantance sahihancin bayanan da ta bayar.
A halin yanzu, ana tsare da mutanen biyu yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da yi musu tambayoyi domin tabbatar da ko su waye, da gano irin ayyukan da suke yi, da kuma ko suna da wata alaƙa da ƙungiyoyin ta’adda.
Operation HADIN KAI ta ce kamen ya nuna yadda ayyukan leƙen asirin rundunar ke taimakawa wajen daƙile shigar mayaƙan ƙasashen waje da kuma ƙarfafa tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar kai sahihan bayanai cikin gaggawa, tana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da ta’addanci da dawo da zaman lafiya.
