<span></span>
A jiya Juma’a aka yi jana’izar manoma 26 da aka kashe a wani hari da ’yan bindiga suka kai a Jihar Zamfara, kamar yadda majiyoyin yankin da wata sanarwa daga hukumomi suka tabbatar.
Hukumomin yankin sun ce an kai wa manoman harin ne a ranar Alhamis, yayin da suke aiki a gonakinsu da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta jihar.
Kisan ya sake tayar da fargaba a tsakanin al’ummomin manoma, inda da dama daga cikinsu suka daina zuwa gonakinsu saboda ci gaba da hare-haren da ƙungiyoyin ’yan bindiga masu ɗauke da manyan makamai ke kai wa a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Yayin wata ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar da abin ya shafa a madadin Gwamna Dauda Lawal, Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mani Malam Mummuni, ya buƙaci mazauna yankin su ƙara haƙuri, yana mai cewa gwamnatin jihar na ci gaba da jajircewa wajen kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
“Gwamna ya aiko ni in ce ku ƙara haƙuri. Ba ku kaɗai abin ya shafa ba. Yana sane da halin da mutanen Zamfara gaba ɗaya ke ciki,” in ji Mummuni.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta shiga tattaunawa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makaman ba.
“Da yardar Allah za mu magance su, amma ba za a yi wata tattaunawa da su ba, domin yaudara ce, ƙarya ce, kuma ta’addanci ne,” in ji shi.
Sabbin kashe-kashen sun faru ne a daidai lokacin da hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da addabar al’ummomin manoma, manyan tituna da ƙauyuka a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Hare-haren sun haɗa da kashe-kashe, sace mutane domin neman kuɗin fansa, satar shanu da sauran munanan laifuka.
TRT Hausa ta ruwaito cewa, wannan hari ya biyo bayan wasu munanan hare-hare da aka kai a cikin makonnin baya.
A watan Yuni, aƙalla manoma 17 aka kashe, yayin da wasu 13 suka jikkata lokacin da aka kai musu hari a gonakinsu da ke Goron Namaye, a Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mazauna yankin 39 da suka taru domin tattaunawa kan yadda za a sako ’yan uwansu da aka sace.
Tun da farko a watan, wani hari da aka kai ƙauyen Gora, shi ma a Ƙaramar Hukumar Maradun, ya yi sanadin mutuwar manoma shida, tare da jikkata kusan mutum 10 da kuma yin garkuwa da wasu mazauna yankin.
Rikicin ya wuce Zamfara kaɗai, domin a cikin ’yan watannin nan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun kai hare-hare masu muni tare da yin garkuwa da mutane da dama a jihohin Katsina, Kaduna, Neja da Sokoto.
Haka kuma hare-haren na ci gaba da yaɗuwa zuwa wasu sassan Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yammacin Najeriya.
A farkon wannan watan, rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa dakarunta, tare da haɗin gwiwar masu aikin sa-kai, sun kashe fiye da mutum 300 da ake zargin ’yan bindiga ne a wani babban farmaki da suka kai a Jihar Zamfara.
Rundunar ta bayyana farmakin a matsayin ɗaya daga cikin manyan hare-harenta na baya-bayan nan kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankin.
Sai dai duk da nasarorin da sojoji ke samu a wasu hare-hare, ƙungiyoyin masu ɗauke da makaman na ci gaba da samun ƙarfi a cikin dazuka masu nisa, inda suke samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu ta hanyar kuɗin fansa, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma satar shanu.
