Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau Alhamis, domin yin bayani a kan ayyukan kasuwanci da yadda aka tafiyar da su a rabin farkon shekarar 2026. Shugabar sashen kula da jarin waje na ma’aikatar kasuwanci ta kasar, Meng Huating ta mayar da amsa ga tambayoyin da suka shafi harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, inda ta bayyana cewa, a halin yanzu, tawagogin kasuwanci na bangarorin biyu suna tuntubar juna game da tsarin kwamitin cinikayya, ayyukansa, da kuma yadda za a gudanar da shi, kana suna tattaunawa kan yadda za su ciyar da shirin rage harajin fito na yi-min-na-rama na dala biliyan 30 ga kowane bangare gaba. Jami’ar ta kuma kara da cewa, bangaren Sin yana sauraron ra’ayoyin masu ruwa da tsaki daban-daban, ciki har da kamfanoni da kungiyoyin kasuwanci na cikin gida, da kananan hukumomin kasar, da kuma kungiyoyin kasuwanci na kamfanonin jarin Amurka da dai sauransu, game da shawarwarin tsarin rage haraji. Shi bangaren Amurka kuma yana neman ra’ayoyin jama’a game da kwamitin cinikayya da kuma ayyukan rage harajin fito. A cewar jami’ar, bangarorin biyu za su ci gaba da tuntubar juna ta kut-da-kut, da gaggauta cimma matsaya kan tsarin rage haraji ga takamaiman kayayyaki tare da inganta aiwatar da shi, da nufin kara fadada cinikayyar da ke tsakaninsu. (Bilkisu Xin)
Uzairu Rajamani
An gano gawar wani ɗalibi mai matakin karatu na 200 a Jami’ar Tarayya da...
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta bayyana damuwa kan...
Kwanan nan, Wang Yi, mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin...
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yaye jami’an tsaro na Marshall su 1,550 a yunƙurinta na...
A shekarun baya bayan nan, jerin sakamakon binciken jin ra’ayoyin jama’a daga cibiyoyi mabanbanta, na kara shaida...
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa kuɗaɗen ajiyar ƙasar a ƙasashen waje sun...
Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, mambobin Ƙungiyar Kawancen Ƙasashen Sahel (AES), sun nuna sha’awar haɗa ƙarfi...
Sanatan Amurka Ted Cruz ya zargi gwamnatin Najeriya da mayar da hankali kan kamfen...
Jam’iyyar ADC ta ce wasikar da aka ruwaito shugaban Amurka Donald Trump ya aike wa Shugaba Bola...
