<span></span>
Cibiyar Kare Haƙƙin Dan Adam da Ilimantar da Jama’a (Resource Centre for Human Rights and Civic Education – CHRICED) ta buƙaci a gudanar da bincike kan taƙaddamar da ta ɓarke kan zargin kafa hukumar bogi a Najeriya.
Haka kuma ta buƙaci a dakatar da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, har sai an kammala bincike.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, cibiyar ta ce zarge-zargen da ake yi kan kafa PFIPC sun haifar da damuwa kan yadda ake tafiyar da gwamnati cikin gaskiya da riƙon amana.
Ta ce wannan ya biyo bayan zargin da tsohon Darakta Janar na kwamitin, Adeniyi Adeyemi, ya yi cewa an taimaka masa wajen ba shi muƙami a gwamnati mai ci “bayan an biya wasu kuɗi.”
CHRICED ta buƙaci a kafa kwamiti da zai yi bincike mai zaman kansa da zai ƙunshi ƙungiyoyin, masu yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma masana shari’a domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan taɓarɓarewar matsalar tsaro a Najeriya, tare da yin kira ga gwamnati ta ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da mulki.
Har ila yau, ta buƙaci gwamnati ta bayyana bayanan dukkanin kwamitoci da hukumomin da ke ƙarƙashinta.
Sannan ta yi kira ga ƙungiyoyi, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da neman jami’an gwamnati su riƙa ɗaukar alhakin ayyukansu.
