<span></span>
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta janye dakatarwar wasa guda da ta ƙaƙaba wa ɗan wasan Amurka, Folarin Balogun, bayan jan katin da ya karɓa.
Matakin zai bai wa Balogun damar buga wasan da Amurka za ta yi da Belgium a gobe Talata.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da matakin na FIFA, yana mai cewa hakan ya gyara abin da ya kira rashin adalci da aka yi wa ɗan wasan.
Balogun ya samu jan kati kai tsaye ne bayan ƙetar da ya yi wa ɗan wasan Bosnia da Herzegovina, Tarik Muharemovic a wasan zagayen ’yan 32, wanda Amurka ta yi nasara da ci 2-0.
Ɗan wasan mai shekara 25 ya zuwa yanzu ya zura ƙwallaye uku a gasar, waɗanda suka taimaka wa Amurka kaiwa wannan mataki.
A cikin sanarwar da FIFA ta fitar, ta ce an dakatar da hukuncin na wasa guda na ɗan lokaci, ba tare da bayyana takamaiman dalilin yin hakan ba.
Hukumar ta yi nuni da tanadin dokokinta da ke ba ta damar sassauta ko dakatar da wasu hukunci idan akwai dalilan yin hakan.
Sai dai FIFA ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa matakin ya biyo bayan shiga tsakani da Trump ya yi ba.
Rahotanni sun ce Trump ya tuntuɓi Shugaban FIFA, Gianni Infantino, kan batun, amma dai babu wata sanarwa daga FIFA da ta tabbatar da cewa wannan ne ya sa aka janye dakatarwar.
Haka kuma, an ruwaito cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Belgium na duba lamarin.
