<span></span>
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɓoye kusan Naira tiriliyan 8.8 na kuɗaɗen gwamnati domin tunkarar Zaɓen 2027.
Atiku ya ce zargin nasa yana da nasaba ne da wani rahoton Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) wanda kuma Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya wallafa a ranar 1 ga Yulin 2026.
Rahoton ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta shigar da bayanan wasu kuɗaɗen gwamnati da suka kai kusan kashi biyu cikin ɗari na tattalin arzikin ƙasar ba wato GDP a cikin kasafin kuɗin baya-bayan nan ba.
A cewarsa, idan aka yi la’akari da girman tattalin arzikin Najeriya da ya kai kusan Naira tiriliyan 441.5, hakan na nufin an kashe kusan Naira tiriliyan 8.8 ba tare da an bayyana su a cikin kasafin kuɗi ba ko kuma jama’a sun san yadda aka kashe su.
Atiku ya bayyana lamarin a matsayin mafi tayar da hankali a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya a baya-bayan nan, yana mai kira ga ’yan Najeriya, kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyin fararen hula, Majalisar Dokoki ta Ƙasa da sauran cibiyoyin dimokuraɗiyya su binciki batun.
Ya ce rahoton IMF, wanda wakilin asusun a Najeriya, Christian Ebeke, ya gabatar, ya nuna cewa giɓin ya samo asali ne daga manyan ayyukan gwamnati da aka aiwatar ba tare da sanya su cikin kasafin kuɗi ba.
A cewarsa, hakan na nuna cewa Gwamnatin Tarayya na gudanar da manyan kwangiloli da ayyukan raya ƙasa na tiriliyoyin naira ba tare da cikakken tsarin sa ido da doka ta tanada ba.
Atiku ya kuma zargi Gwamnatin Tarayyar da cire Naira biliyan 800 daga kuɗaɗen da ya kamata a raba wa gwamnatocin jihohi ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa ko umarnin kotu ba.
Ya yi zargin cewa haɗa wannan Naira biliyan 800 da kuma Naira tiriliyan 8.8 da ake cewa ba a shigar da su cikin bayanan kasafin kuɗi ba na nuna ana gina wata babbar taskar kuɗi domin tunkarar Zaɓen 2027.
