<span></span>
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ɗaukai nauyin tura ɗalibai 22 ’yan asalin jihar domin karatu a ƙasashen Indiya da Pakistan.
Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ne ya bayyana hakan yayin bikin yi wa sahun farko na ɗalibai 22 bankwana kafin tafiyarsu zuwa ƙasashen Indiya da Pakistan domin karatu a fannoni daban-daban.
Ya ce gwamnatin za ta ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ’yan asalin jihar da suka cancanta a ƙasashen waje domin ƙara inganta ƙarfin ma’aikata a fannoni masu muhimmanci.
Gobir ya ce shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da ƙwararrun ma’aikata a fannonin da ake da ƙaranci, ta hanyar ɗaukar nauyin karatun kwasa-kwasan da ba a koyar da su a Najeriya.
Ya buƙaci ɗaliban da su kasance jakadu nagari na jihar da ƙasar Najeriya a ƙasashen da za su yi karatun, sannan su guje wa duk wani abu da ka iya jefa su cikin matsala.
Haka kuma, ya shawarce su da su mayar da hankali kan karatunsu domin tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnati ta kashe wajen tallafa musu sun samar da sakamakon da ake buƙata.
Tun da farko, Babban Sakataren Hukumar Ba da Tallafin Karatu ta Jihar Sakkwato, Alhaji Kabir Labaran, ya yabawa gwamnatin jihar bisa ƙoƙarinta na bunƙasa ilimi.
Ya ce gwamnatin Gwamna Ahmad Aliyu ta biya biliyoyin nairori na bashin tallafin karatu da ta gada daga gwamnatin da ta gabata, wanda ya shafi ɗaliban jihar da ke karatu a manyan makarantu a Najeriya da ƙasashen waje.

