<span>Mai Shaho riƙe da wani bunsuru da ya binne da rai.</span>
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta nesanta kanta daga ayyukan wani boka da aka fi sani da Mai Shaho, bayan wani faifan bidiyo ya nuna shi yana iƙirarin cewa zai ba Gwamna Ahmad Aliyu nasara a Zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Gwamnatin Jihar Sakkwato, Abubakar Bawa ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da mutumin ko kuma ayyukansa, duk da cewa ya bayyana goyon bayansa ga jam’iyyar APC.
A wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, wanda ake zargin Mai Shaho ne ya fitar, an gan shi yana binne bunsuru da rai, yana iƙirarin cewa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC, Manir Muhammad Ɗan’iya, ba zai samu karɓuwa a wajen masu zaɓe ba, don haka ba zai yi nasara ba.
Gwamnatin jihar ta ce ba ta da wata alaƙa ko dangantaka da mutumin, kuma ba ta goyon bayan bokaye ko masu sihiri, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke mara wa baya ba.
Ta kuma jaddada cewa ba ta da hannu a ayyukan da aka nuna a cikin faifan bidiyon, kuma ba za ta amince da duk wani aiki da ya saɓa wa doka, ɗabi’a da koyarwar addinin Musulunci ba.
A cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce: “Jihar Sakkwato jiha ce da mafi yawan al’ummarta Musulmai ne, kuma mutanenta suna riƙe da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), da tafarkin Sahabbansa, tare da bin koyarwar Mujaddadi Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo. Saboda haka, gwamnatin jihar ba za ta amince da duk wani aiki da ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci ba.”
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta yi kira ga duk masu aikata bokanci da sauran ayyukan da suka saɓa wa koyarwar addinin Musulunci da su ji tsoron Allah su daina.
Haka kuma, ta bayyana cewa an umarci Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato da ta ɗauki matakin da ya dace bisa tanadin doka kan lamarin.
