<span></span>
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta rufe shafinta na karɓar sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu na Zaɓen 2027 bayan wa’adin da ta ƙayyade ya cika.
Wani babban jami’in INEC, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin magana a hukumance, ya shaida wa Aminiya cewa jam’iyyun da abin ya shafa sun haɗa da APGA, sai PDP tsagin da Nyesom Wike ke jagoranta, da kuma tsagin LP da Nenadi Usman ke jagoranta.
Sai dai jami’in ya ce kusan duk sauran jam’iyyun masu rajista ciki har da APC, ADC, da NDC sun kammala shigar da sunayen ’yan takararsu kafin wa’adin ya ƙare.
Ana sa ran bayan rufe shafin karɓar sunayen, INEC za ta fara tantance sunayen da ta karɓa a shafin da aka ɗora sunayen bisa tanadin Dokar Zaɓe da ƙa’idojin hukumar.
A ranar Lahadi ne INEC ta sanar da tsawaita wa’adin gabatar da sunaye da takardun shaidar ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya daga ranar Asabar, 11 ga Yuli, zuwa tsakar daren Talata, 14 ga Yuli, bayan roƙon da wasu jam’iyyu suka yi.
Daga cikin jam’iyyun da suka yi nasarar gabatar da sunayensu akwai APC, wadda ta gabatar da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima domin neman wa’adi na biyu; sai ADC, wadda ta gabatar da Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi; da kuma NDC, wadda ta gabatar da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Majiyoyi daga INEC sun kuma bayyana cewa wasu jam’iyyu sun gabatar da sunan ɗan takarar shugaban ƙasa ne kawai ba tare da sunan mataimakinsa ba.
Haka kuma, yayin da ake ci gaba da ɗora sunayen ’yan takara kai tsaye a shafin INEC, har yanzu ana fuskantar ruɗani a wasu jihohi, ciki har da Binuwe, Kwara da Nasarawa, kan waɗanne sunaye ne a ƙarshe suka samu shiga a matsayin ’yan takarar Majalisar Dattawa da ta Wakilai.
