<span>Gwamnan CBN Yemi Cardoso</span>
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa kuɗaɗen ajiyar ƙasar a ƙasashen waje sun ƙaru zuwa dalar Amurka biliyan 52.73, daga dala biliyan 48.88 da aka samu a watan Janairu.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana hakan ne yayin gabatar da rahoto a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin bankuna da inshora.
Ya danganta wannan ci gaba da ƙarin amincewar masu zuba jari da sauye-sauyen manufofin tattalin arziƙi.
Gwamnan ya kuma ce adadin kuɗaɗen ajiyar da ƙasar za ta iya amfani da su kai tsaye ya haura dala biliyan 40, bayan da ya kasance kusan dala biliyan huɗu a shekarar 2023.
Sai dai Shugaban Kwamitin, Sanata Adetokunbo Abiru ya ce ƙara ƙarfin bankuna ya kamata ya haifar da sauƙin samun rance ga sassan noma, masana’antu, fasaha da ƙananan sana’o’i domin al’umma su amfana.
